Hukuma Ta Nuna Gamsuwa Da Nasarorin Magance Zaizaiyar Kasa A Gombe

0
67

Hukuma Ta Nuna Gamsuwa Da Nasarorin Magance Zaizaiyar Kasa A Gombe

Daga Khalid Idris Doya, Gombe

Jami’i mai kula da ayyukan hukumar magance zaizayar kasa da alkinta ruwa ta Nijeriya wato NEWMAP Dakta Salisu Dahiru, ya yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da kyakkyawan shugabancin da ya dace da sakin kudaden hadaka da sauran tallafi ga hukumar ta NEWMAP a Jihar Gombe don aiwatar da aikin dinke kwarin Jami’a mallakar Jiha zuwa Malam Inna dama ayyukan farfado da dazuka a fadin jihar.

Dakta Dahiru wanda ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ya duba yadda aikin kula da zaizayar kasa na Malam Inna ke gudana, ya nuna gamsuwa da ingancin aikin da ake gudanarwa.

Ya ce NEWMAP a Jihar Gombe ta yi rawar gani ta fuskar aiwatar da ayyukan da aka sa a gaba, yana mai cewa ingancin aikin na Jami’ar Jihar Gombe da ke gudana zuwa Malam Inna ya kasance mai gamsarwa sosai duba da saurin aikin wanda da farko aka tsara yin sa cikin watanni 18 amma yanzu zai kammala cikin watanni 7 kacal.

Yayin da ya ke yaba wa masu ruwa da tsaki bisa rawar da suke takawa wajen aiwatar da aikin, musamman shugabannin al’umma saboda hadin kan da suka bayar wanda ya zama silar nasarar aikin. Jami’in ya yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon bayan da duk ake bukata don saukaka aiwatar da sauran ayyukan da aka tsara yi kafin kawo karshen shirin.

A sport da tsare-tsaren da ake yi na daurewar ayyukan ko da bayan karewar shirin na NEWMAP, ya ce tuni Bankin Duniya ya samar da wani shirin kyautata noma da muhalli mai suna ACReSAL a takaice, wanda za a jingina shi kan tsarin na NEWMAP don ci gaba, ya kara da cewa Jihar Gombe tana da duk abin da ake buƙata don shiga cikin sabon shirin.

A jawabinta, Kwamishiniyar muhalli da albarkatun gandun daji, Dakta Hussaina Danjuma Goje ta yaba wa jami’in hukumar ta NEWMAP bisa jagoranci da tallafin sanin makama da yake bayarwa ga hukumar a Jihar Gombe wadanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da manufofin shirin.

Ta kuma tabbatar wa sauran al’ummomin da ke fuskantar barazanar zaizayar kasa da sauran kalubale na muhalli cewa wannar gwamnati za ta kawo musu tallafi kamar yadda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ke kokarin magance kalubalen muhalli a jihar.
Da ya ke jawabi tun da farko, jami’in kula da ayyukan hukumar ta NEWMAP a Jihar Gombe, Injiniya Muhammad Garba ya bayyana cewa aikin dinke kwarin na Jami’ar Jihar Gombe zuwa Malam Inna ya kai tsawon kilomita 7 da rabi kuma yanzu ya kai kaso 75 cikin dari na kammaluwa.

Ya ce, NEWMAP za ta yi hadin kai da dan kwangilan domin duba yiwuwar gina madatsar ruwa da zata rika tara ruwan dake kwarara yana haifar da ambaliya don yin amfani da shi a ayyukan gona da sauran ayyukan.

Shi ma da yake jawabi, mai baiwa Gwamnan Shawara na Musamman kan Kasafin Kudi, Tsare-tsare da alaka da abokan hulda, Dakta Ishiyaku Muhammad, ya ce an samar da tsare-tsare da manufofin da za su kare muhalli a cikin tsarin ci gaban shekaru 10 na jihar, yana mai bayar da tabbacin cewa Gombe za ta ci gaba da shiga Bankin Duniya da sauran kungiyoyin bada tallafi na duniya don samar da kyakkyawar mafita kan inganta muhalli.

Dagatan Malam Inna da Kagarawal, Haruna Mohammed Bose da Usman Bello, solar bayyana cewa aikin dinke kwarin Jami’ar Jihar Gomben zuwa Malam Inna shine aiki mafi muhimmanci da aka taba aiwatarwa a anguwannin saboda ya taimakawa fiye da mutane dubu 100 dake rayuwa a bakin kwarin.

Shugabannin biyu solar tabbatar da cewa mutane da dama solar amfana da aikin kai tsaye ta hanyar samun ayyukan yi da ya kai ga inganta rayuwar su.

Ko’odinetan shirin na kasa, wanda ya zo jihar bisa gayyatar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya tattauna da Gwamnan a ofishin sa kan magance matsalolin muhalli a jihar. A yayin taron, Gwamna Inuwa ya tabbatar wa jami’in cewa Jihar Gombe ta dukufa ka’in da na’in wajen cika ka’idojin samun damar shiga shirin na ACReSal wanda shi ne zai maye gurbin NEWMAP.

Ya ce Jihar Gombe a shirye take ta yi duk abinda ya dace na tabbatar da fara shirin duba da tasirin da hakan zai yi ga rayuwa da sana’o’in jama’a.

What's On Your Mind?