Hujjarmu Ta Yin Idin karamar Sallah A Jiya –Sheikh Dahiru Bauchi

- Advertisement -

Hujjarmu Ta Yin Idin karamar Sallah A Jiya –Sheikh Dahiru Bauchi

Daga Khalid Idris Doya,

A jiya ne dubun dubutar mabiya Shaikh Dahiru Usman Bauchi suka gudanar da Idin karamar Sallah a Bauchi bisa jagorancin shehin malamin.

Massalatan solar fara taruwa tun daga karfe bakwai na safiya har zuwa karfe goma na jiya inda suka tsaida Sallar Idin mai raka’a biyu a gidan Shaikh Dahiru Usman Bauchi da ke kan hanyar Gombe a cikin garin Bauchi.

An yi Khudubar Idi da kuma sauran jabawan da suka gabata, inda babban dan Shehin, Malam Ahmad Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi ya gabatar da Sallar bisa umurnin Sheikh Dahirun.

A cikin hudubarsa ya jawo hankalin jama’a dangane da jin tsoron Allah cikin lamura tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar nan.

Ya hori al’umma da su kasance masu jin tsoron Allah a kowani lokaci, yin abun da Allah ya ce da hani ga abun da ya hana, kana ya tunatar dangane da Fidda kai da musulmai ke yi, tare da jawo hankali kan kyawaan dabi’un da za su kai ga taimakon bawa.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida bayan gabatar da Sallar Idin, Babban Malamin na Tijjaniya a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar solar ajiye Azumin watan Ramadana ne bayan da suka tabbatar da ganin watan Shawwal daga adilan mutane.

Ya kuma bayyana cewar batun Azumin watan Ramadana yana nan a cikin addini bisa koyarwar Manzon Allah (SAW) don haka suke bin umarnin Annabi, “Duk abun da ka ga ana yi a addini, Annabi ne ya karba wa mutane, idan Annabi ya yi magana to maganar kowa ta kare, maganarsa kawai ake ji, ba a jin maganar kowa, daga maganar Allah sai Annabi da yake mana tarjama. To Annabi ya ce, “Idan kun ga watan Ramadana ku kama Azumi, idan kuma kuka ga watan Shawwal ku ajiye Azumi, idan kuma watan Azumi ya kare ba ku ga wata ba sai ku cika Azumi zuwa 30, idan kuma wata bai buya ba an ganshi mene ne uzuri?.

“Kuma ba mu da ikon mu karyata wadanda suka ce solar ga wata din nan. Akwai wadanda solar ga watan Shawwal a Bauchi, ni dai kaina ma na ga mutumin da ya gani, an gani Gombe, an gani a Gadau, an gani a Argungu, da sauran garuruwa ba za mu karyata duk wadanda nan kawai mu ci gaba da Azumi a watan Shawwal.”

Ya ce su da suke da hujjarsu na yin Sallah a ranar Laraba wadanda basu yi sallar ba suma suna da nasu hujjar na daban, “Mu abun da ya sanya muka yi sallah a yau (Jiya Laraba) muna da hujjarmu, su ma abun da ya sanya ba su yi sallah ba suka ci gaba da Azumi suna da hujjarsu ba mu san wacce iri ce ba.”

Ya kuma bayyana cewar dukkanin matakan da suka dace wajen ganin solar sanar da Sarkin Musulmi Sa’advert Abubakar dangane da cewa an ga watan Shawwal a ranar Talata solar bi biyo bayan da shi din ya amince tare da tabbatar da ganin watan, “Na buga waya na samu Sarkin Malaman Sokoto na ce ka-ji-ka-ji amma ka san yadda za ka isar wa Sarkin Musulmi, ya tabbatar min da cewa Insha Allahu zai isar, sannan kuma akwai wani ma’aikacinsa, masoyinsa, abokin aikinsa Sarkin Kafin Argungu shi ma na buga masa cewa ga shi mutane solar kawo min labarin solar ga wata wanda ni na yarda da shi, a kuma fada wa Sarkin Musulmi an ga wata. Shi ma ina tsammani zai gaya masa.”

Har-ila-yau, ya kuma bayyana cewar matakan da suka dace duk su isar wa Sarkin Bauchi shi ma solar bi domin ganin solar isar da sakonsu ga wadanda suka dace.

Dangane da rikita-rikitan ganin wata da ake samu a shekaru da dama a Nijeriya, Shehin ya bayyana cewar mafitar guda ita ce a bi abun da Allah da Annabi suka ce, “Matakai kawai sai bin maganar Annabi (SAW) a bi maganar Annabi kawai da yake cewa, ‘In kun ga wata ku kama Azumi, In kun ga wata ku ajiye Azumi. In ko ya kai kwana 29 baku ganshi ba sai ku cika zuwa 30. to an riga an ganshi ya aka iya? Mafitar a koma ga maganar Annabi.”

Haka nan ya tabo batun da wasu ke yi na cewa ana kokarin daidaita ganin watan Nijeriya da na kasar Saudiyya, inda Shehi Dahiru ya bayyana cewar “Wannan ai jahilci ne yanzu lokacin da Saudiyya suka yi Sallar secure nan mu za mu yi? Ai dare ne lokacin, da Saudiyya suka yi sallar Azahar za mu yi? Ai lokaci bai yi ba hantsi ne a wajenmu, lokacin da suka yi La’asar za mu yi? Lokacinmu bai yi ba don kusan Azahar ne a nan, lokacin da za su yi Magriba rana ta fadi a wajensu mu kuma muna ganin rana kwal sai mu yi sallar magriba don saudiyya ta yi?” ya taimabaya.

Dangane da matsalar tsaro, babban malamin ya yi addu’ar Allah zaunar da kasar nan lafiya tare da kira ga hukumomi da su kara azama wajen kare rayuka da dukiyar jama’a, yana mai cewa matsalar tsaro na masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga gami da ‘yan Boko Haram matsaloli ne da suke neman wuce gona da iri wanda ya nemi hukumomi su kara kokari domin kawo karshen hakan.

“Mun sha fada cewa gwamnati ta fi kowa ido ta fi kowa kunne duk abubuwan nan da ake yi ta fi kowa gani, ta fi kowa jin me ke faruwa, sai dai abun bakin ciki ba a yi maganin abun ba har yanzu, kullum ana sace mutane a je a sayar, kullum ana kashe mutane, kullum ana kona gidajen mutane, da kayan abincinsu babu zaman lafiya ko ina da ina.

“Duk matsalolin tsaron nan ga su suna nan ita ma gwamnati tana nan, kuma dama amfanin gwamnati shine ta kiyaye rayukan jama’anta ta kiyaye dukiyarsu.”

Daga karshe ya nemi jama’a da su dukufa yi wa kasa addu’a tare da komawa ga Allah a kowani lokaci domin neman tsira duniya da lafiya.

 

- Advertisement -