Hotunan jami’an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna (Kano)

0
102

Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kano solar tirsasa matasa inda suka dinga aske musu gashin kansu sakamakon askin da suka yi ba na Musulunci ba.

Sau da yawa jami’an hukumar Hisbah suna damke matasa a jihar Kano a kan laifin saka kaya ba yadda ya dace ba.

Su kan tsare masu adaidaita sahu da ke ado da hotunan mawaka ko jaruman fina-finai.

Lamarin nan da ya faru ya janyo cece-kuce daga kafafen sada zumuntar zamani.

A wani labari na daban, wata kotun rundunar soji da ke zama a Maiduguri jihar Borno a ranar Laraba, ta kori wani soja daga aiki tare da yanke masa hukuncin zaman shekaru 5 a gidan yari.

Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu ‘yan ta’adda a Borno

Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Sojan mai suna kofur, Aliyu Yakubu an kama shi da laifin yin fyade a ranar 13 ga watan Yulin 2020 kuma an gurfanar da shi a gaban kotun sojin.

Kamar yadda soja mai gabatar da kara ya sanar, Yakubu ya ja yarinya mai shekaru 13 zuwa wani kango a ranar 1 ga watan Yulin 2018 a Bama inda ya ci zarafinta kafin ya yi mata fyade.

Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Yarinyar ta sanar da kotun cewa, sojan yayi mata fyade ne yayin da ta bar gidan kanwar mahaifiyarta za ta tafi gidansu.

“Ya tambayeni inda zani kuma na sanar masa, daga nan ya ja hannuna yace in bi shi,”lauya Aminu Mairuwa, mai mukamin Kaftin ya sanar kamar yadda yarinyar tace.

“Ya ja ni zuwa wani kango ta bayan tsohuwar gidan yari sannan ya rufe min baki saboda ina ihu.

“Ya fito da wuka tare da yin barazanar kasheni. Bayan ya yi min tsirara sai ya kasa shigata. Daga nan ya tambayeni ko an taba saduwa da ni, amma nace a’a. A take ya shigeni ta karfi.

“Bayan kammala fyaden, ya yi amfani da bulo wurin fasa min kai kuma ya bar ni ban san halin da nake ciki ba,” cewar Mairuwa.

What's On Your Mind?