Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun amarya Nwakaego sun janyo masa caccaka

0
137

Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun amarya Nwakaego sun janyo masa caccaka

Dan gwamnan Jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya sake fitar da wasu sabbin hotunansa tare da matar da zai aura mai suna Halima Nwakaego Kazaure.

Bello ya wallafa hotunan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata 17 ga watan Nuwamban 2020.

Hotunan sun nuna Bello tare da Nwakaego a wani wuri mai kyau tare da furanni a bayansu sun kuma riko juna.

Irin wannan yanayin da suka dauki hotunan ya janyo cece-kuce musamman a shafin Twitter inda wasu da dama suka janyo hankalin Bello cewa abinda ya yi ya saba wa koyarwar addinin musulunci har ma da al’addar bahaushe dan arewa.

Allah yayiwa Mahaifin Margayi Sheikh Albani zaria Rasuwa

Ko a kwanakin baya ma Bello El-Rufai ya fitar da wasu hotunan biyu tare da suka dauka tare da sahibarsa Halima Nwakaego.

Wasu mutanen kuma suna ganin bai dace a tsaya ana bata lokaci a kan hotunan da ya wallafa a a yayin da matsaloli irin na tsaro da sauransu na addabar mutane.

Ga dai wasu daga cikin ra’ayoyin mutane da suka yi tsokaci a shafin na Twitter.

@AbdulMalumfashi1 ya ce, “Kaji tsoron Allah Bashir. Wannan hoton bai dace dakaiba.

@oluwatosinodun2 ya ce, “Ina takaicin yadda aka hada ni kasa daya tare da irinku. A maimakon ku mayar da hankali kan yi wa shugabanni magana recreation da rashin tsaro kun fiye damuwa da abinda wani ke yi a rayuwarsa. Duk abinda mutum ya ga daman bautawa matsalarsa ne.

@Kaneem7 ya ce, “A lokacin da @Rahma_sadau ta wallafa hotuna, kun yi ta mata fada amma yanzu babu wanda ke magana… Ina muku fatan alheri.

@BABANZAURE22 ya ce, “Fada alheri ko kayi shiru. Me yasa zaka yanke hukunci bayan Allah ne Alkalin Alkalai.

@soltan212 ya ce, “Saba dokokin Allah da Manzonsa ba zai haifar maka alheri a aurenka ba. Kana bukatar albaraka Allah a gidanka fiye da yabon da mutane za suyi maka. Ya Allah ka yi magana jagoranci @hadizel

Tattara wannnan bayyanai mun samu shine daga jaridar Legit.

Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun amarya Nwakaego sun janyo masa caccaka

What's On Your Mind?