HOTUNAN: Alan Waka Ya Fadi Lokacin Da zai ƙaddamar Da Diwanin wakokinsa

0
123

Da lokaci yayi za a sanar da gayyata cikin yardar Allah.”

Shahararen mawakin nan Aminu Abubakar Ladan Wanda ake fi sani da alan waka wanda yayi littafi sukutum na diwanin wakokinsa wanda kuma za’a fitar da shi nan gaba kadan inda ya nuna cewa a bayan sallah zai kadamar da wannan littafi

Subhannallah Kalli Video Yadda Aka Zana Tatoo A Bayan Jarumar Film Din Hausa

“Za a ƙaddamar da wannan DIWANIN WAƘOƘIN ALA Bayan Sallah da ƙarfin Allah.

Da lokaci yayi za a sanar da gayyata cikin yardar Allah.”

Wanda jarumin yayi godiyaga Allah akan bisa samun damar yin wannan littafi inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta kamar haka.

“Muna Jaddada godiya ga Allah domin tarin Ni’imomi tare da Yassarewa da sahalewa ta irin wannan Nasibi abin bugun gaba a raye da bayan wafati.

Haƙiƙa wannan kundi wata manuniya ce ta sakamakon Nagarta da Jajircewa.

Ashe Martaba da mutunci suna daga abin nema acikin rayuwar tauraro ba KANKAJERE a wajen neman garin kuɗi ta kowanne hali ba.

Sai nake ganin abin kamar wata WAIBUWA irin yarda martabobi ke jeren farin dango kamar ana tisa ƙwayar carbi.

ALHAMDU LILLAHI RABBUL ALAMINA!!!
Babu furuci na yabo da godiya sama da wannan. A ƙarshe ina miƙa godiya ga Marubuta wannan Littafi na DIWANIN WAƘOƘIN ALA, Da suka sami ikon hattama wannan Kundi tin ina Raye.

Ina shaidawa Masoya da Manzarta cewa za a kaddamar da wannan littafi da karfin Allah a jihar kanon Dabo, Bayan Sallah da izinin Ubangiji kowa.

Allah ya bada ikon Halartar wannan Gagarimin taron Kaddamarwa da za a yi a kano daga zarar an saka lokaci za a shaida maku masoya na haƙiƙi.”

What's On Your Mind?