Hotuna Matar Data Haifi ‘Ya ‘Ya Gome Ita Da Mijin Ta Wa Yafi Kokari..?

- Advertisement -


Wannan Labarin Gaskiya Ne Domin Hakan Ya Faru, Ga Dai Yadda Labarin Yake A Rubuce Tare Da Hotuna.

Mijin matar da akace ta haifi yan 10 a Afrika ta Kudu ya bawa jama’a hakuri cewa karyane shima bai taba ganin jariran ba.
Mijin matar nan ƴar Afirka Ta Kudu da akace ta haifi ƴan 10 ya yi amai ya lashe inda yace gaskiyar magana karya matarsa ke yi bata haifi yan 10 ba kamar yadda tace kuma shima bai taba ganin jariran da tace ta haifa ba.

Manuniya ta ruwaito Mijin matar mai suna Gosiame Thamara Sithole ya fitar da sanarwar cewa jama’a su daina tura gudunmuwa ga jariran domin babu su.

A cewar mijin nata mai suna Teboho Tsotetsi dama matar tasa ce ta kira shi a waya take sanar dashi cewa ta haifi yan 10 maza bakwai mata uku. Amma tun daga ranar bata yarda yaje inda take ba balle ya ga jariran kuma taki fada masa inda take. Yace tun suna kiranta a waya tana dauka har ta kai ga yanzu ma ta daina daga waya kana wayarta a kashe.

Ms Sithole, mai shekara 37, a baya ta haifi ƴan biyu, waɗanda a yanzu shekarunsu shida. Sai dai mijin nata wanda yace dama budurwarsa ce basuyi aure ba tukunna ta bata ko kasa ko sama sun neme ta sun rasa kuma har sun bawa rundunar yan sanda cigiya.

- Advertisement -