HOTUNA: Kira Ga Masu Fada A Ji A Musulunci :Ya Kamata Su Dakatar Da Wannan Mai Shiga Rigar Musulunci Yana Aikata Baɗala

0
112

Na yi matukar mamakin yadda manyan malamai suka yi burus suka yi shiru suna kallon wata baraka dake ta afkuwa, wani la’ananne ya je sai shiga rigar musulmi yake yana yaɗa baɗala da sunan wai barkwanci.

An samu wani kasurgumin arne mai suna Nedu Wazobia, ko kuma Ofisa Jatau yana shiga cikin rigar musulunci yana yaɗa baɗala. Lallai wannan kalubale ne gare mu musulmai a ce muna barin irin waɗannan la’anannun suna aikata wannan alfahasha da shiga mai girma sannan da suna mai girma.

Nedu Wazobia yana amfani da sunan musulmi da shigar musulmi yana fidda bidiyo marasa kyan gani, yana fidda bidiyo wanda yake baiyana iskanci a cikin su.

Nedu Wazobia yana amfani da sunan Alhaji Musa a cikin bidiyoyinsa, yana yin shiga ta kamala, wadda muke amfani da ita wajen zuwa sallah, yana saka jallabiya fara da hula tare da hirami.

Sunan Musa suna ne mai matukar girma a cikin addinin mu, haka kuma shigar jallabiya da hula da hirami shiga ce ta kamala acikin addinin mu, lallai ya kamata malaman mu su takama wannan katon Arnen burki akan abubuwan da yake na batama Addininmu solar.

What's On Your Mind?