Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

0
171

Dino Melaye, tsohon sanata da ya taba wakiltar yankin Kogi na yamma, ya darzo sabuwar motar kirar Lamborghini Aventador Roadstar.

Tunde Ednut ne ya wallafa hotuna tare da bidiyon motar alfarmar a shafinsa a ranar Asabar da ta gabata.

Fitaccen sananne a shafukan sada zumuntar ya wallafa hoton tsohon dan majalisar yana tuka motarsa mai darajar dala miliyan daya wanda yayi daidai da N460,000,000.

Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

“Sanata Dino Melaye ya siya sabuwar mota kirar Lamborghini Aventandor Roadstar kirar 2020. Kamfanin solar fitar da ita ne a bikin cikarsu shekaru 50. Wannan tana daya daga cikin guda 100 da kamfanin suka yi su a kan dala miliyan 1,” ya wallafa a Instagram.

Ansaki Video Nura M Inuwa Yanayi Ma Wata Kiss A Wajen Dinner Wannan ba Nura M Inuwa Bane Shine Maganar Gaskiya

A watan Maris da ya gabata, tsohon sanatan ya koka da tarin dawainiyar da ke kansa duk da hotunan katafaren gidansa da ya wallafa nasa a kasar ketare.

“Ku taya ni dauka, ku taya ni dauka. Dawainiyar da ke kaina suna karuwa, bakina yana kara fadi,” Melaye yace a harshen Yarabanci.

A wani labari na daban, hotuna da bidiyon katafaren gidan Dino Melaye da tsadaddun kayayyakinsa solar bayyana a yanar gizo.

Wani babban dan jarida kuma dan kasuwa, Dele Momodu ne ya wallafa bidiyon a lokacin da ya kai ziyara tare da zagawa lungu da sako na gidan.

An gano Dino yana kewayawa da Momodu a gidan nasa mai kama da aljannar duniya da ke Abuja, inda ya nuna masa tsadaddun agogunan hannu, takalma, turarruruka, motoci, madafi, wajen cin abinci da sauransu.

What's On Your Mind?