Hotuna : An kashe tsageran IPOB da suka kashe Ahmed Gulak, Kalli gawarwakinsu kwance

- Advertisement -

Jami’an tsaro a jihar Imo sun bi sahun ‘yan Bindiga da suka kashe Ahmed Gulak wanda tsohon hadimin Tsohon Shugaban kasa ne, Goodluck Jonathan a jihar Imo.

Wata Majiyar tsaro ta bayyanawa hutudole.com cewa, jami’an tsaron sun yiwa direban dake tuka motar da Aka kashe Ahmed Gulak a ciki tambayoyi inda ya bayyana musu kalar motocin da ‘yan Bindigar suka je a ciki.

Sun bi sahunsu, kuma sun riskesu a daidai mahadar Afo Enyi dake karamar hukumar Same inda suka tare wata motar data dauko albasa daga Arewa, suke rabawa mutanen gari.

Ko da suka ga jami’an tsaro, sai suka bude musu wuta, an yi musayar wuta dasu, a karshe aka kashe 3 daga ciki, 7 suka ji mumananan raunuka, suka kuma tsere cikin daji. An kuma kona morocinsu 3 da kwace makaman AK47 3 da harsasai da sauransu.

Ana ci gaba da bincike dan gano sauran ‘yan Bindigar da suka tsere.

- Advertisement -