Hisbar Kano Ta Yada Kwallon Mangwaro Kan Jami’inta Da Ya Yi Abin Kunya

- Advertisement -

Hisbar Kano Ta Yada Kwallon Mangwaro Kan Jami’inta Da Ya Yi Abin Kunya

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Hukumar Hisba Ta Jihar Kano ta yada kwallon mangwaro don ta huta da kuad inda ta sallami guda daga cikin manyan jami’anta mai suna Sani Nasidi Uba wanda aka fi sani da Sani Remo bisa zargin jangwalo mata abin kunyata.

Jawabin haka na kunshe cikin takardar da jami’in da ke lura da harkokin ma’aikata na hukumar, Sani Alasan ya rattaba wa hannu kuma aka aike wa MOBILIZED9JA A Yau.

Kwamitin da babban Kwamandan Hukumar ta Hisba Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina ya kafa, ya samu Sani Uba Nasidi da laifin da ake zarginsa da shi dumu-dumu.

Uba, wanda ya shahara wajen kamen karuwai da ‘yan mata masu yawon ta-zubar, a watan Fabarairun wannan shekara aka kama shi da matar aure a dakin otal a sabon gari da ke birnin Kano.

Daga baya wasu jami’an hukumar solar sanar da rundunar ‘yan sandan Jihar Kano cewar matar ‘yar uwarsa wadda ke da matsàla da mijinta. A cewarsa, ya ajiye ta dakin Otal din ne har zuwa lokacin da za a warware matsalar.

Babu dai wani karin bayani kan mataki na gaba da hukumar za ta dauka bayan sallamar sa.

 

- Advertisement -