Hisbah ta cafke mata 19 a Kano da laifukan baɗala

0
13

Babban kwamandan Hisba na Jihar Kano, Dakta Haruna Ibn Sina, ya ce hukumar ta kama mata 19 a jihar da laifukan badala daban daban a kwaryar birnin Kano, The Punch ta ruwaito.

Kwamandan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da Malam Lawal Ibrahim, kakakin hukumar ya fitar a ranar Laraba.

Ya ce an kama matan ranar 19 ga Janairu, da misalin karfe 9:00 na dare a Nasarawa Park lokacin da suke shan kayan maye a titin Ahmadu Bello.

Ya ce sunyi kamen ne biyo bayan umarnin gwamnatin jihar na rufe gidajen kallo da wuraren taro don kauracewa yaduwar COVID-19 a jihar.

Hisbah ta cafke mata 19 a Kano da laifukan baɗala

Na karbi kudin fansa Milyan biyar 5m a hannun tsohon saurayina bayan nayi garkuwa dashi – Inji Budurwa Maryam

“Duk wanda aka kama mata ne kuma solar haura shekara 20.

“18 daga ciki ba a taba kama su ba, daya kuma an taba kama ta,” a cewar sa.

Ya shawarci iyaye da su daina siyawa yayan su manyan wayoyi, su kuma basu tarbiya mai kyau.

A wani rahoto an mika wanda aka kama a karon farko ga iyalan su tare da gargadi, dayar kuma za a bata kulawa ta musamman.

Kamfanin dillancin na kasa (NAN) ta ruwaito an haramta ayyukan badala a karkashin shari’ar musulunci a Jihar Kano.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma’aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Day by day Belief ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

 414 total views,  3 views today

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here