#ENDSARS: Hillary Clinton – Ku daina kashe masu zanga zanga

- Advertisement -

Tsohuwar ƴar takarar shugabancin ƙasar Amurka Hillary Clinton ta yi ƙira ga shugaba Muhammadu Buhari da rundinar Sojoji da su daina kashe masu zanga zanga a jihar Lagos.

Bidiyo: Tirkashi Kalli Mai Sana’a Yana Neman Taimako A Masallaci

Hillary Clinton ta bayyana haka ne a sakon da ta walafa a shafinta na Twitter a cikin wannan dare biyo bayan jami’an tsaro da suka farwa masu zanga zanga a Lekki Tall gate da suka yi kunnen ƙashi da umarnin gwamnati na kafa dokar ta baci.

“Ina ƙira ga Muhammadu Buhari da rundinar Soji da su daina kashe matasa dake zanga zangar EndSars”.

Hillary Clinton - Ku daina kashe masu zanga zanga

Sai dai tuni ta fara shan zafafan martani daga wasu ƴan Najeriya inda wasu dag cikin su ke cewa, “ina take a lokacin da masu zanga zangar ke ƙona dukiyoyin al’umma da gwamnati har ma da kashe jami’an tsaro a jihar Lagos”.

- Advertisement -