Hazard Ya Baiwa Magoya Bayan Real Madrid Hakuri

- Advertisement -

Hazard Ya Baiwa Magoya Bayan Real Madrid Hakuri

Daga Abba Ibrahim Wada

dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Eden Hazard ya bai wa magoya bayan kungiyar hakuri sport da dariyar da ya yi bayan an cire kungiyar daga kofin zakarun turai na Champions League na bana.

An ga tsohon dan wasan na Chelsea mai shekara 30 na wasa da dariya da tsofaffin abokan wasansa na kungiyar Chelsea  bayan an tashi daga wasa lamarin da ya haifar da cece kuce a shafukan sada zumunta.

“Ba ni da niyyar batawa magoya bayan Real Madrid domin ko da yaushe burina na bugawa Real Madrid wasa kuma na zo nan ne domin samun nasara “.

A cewar Hazard a shafinsa na Istagram
An cire Hazard ne kafin a tashi daga wasan bayan ya gaza tabuka komai a kwallon, wanda Real Madrid ta sha kashi da ci biyu babu ko daya wanda hakan ya kai sakamkon wasan Three-1 ba ki daya gida da waje.

Hazard da ya bar Chelsea ne a shekarar 2019, sai dai yana ta fama da suka daga magoya bayan Real Madrid saboda rashin kokari kamar yadda suka yi tsammani, wasu ma na kiran cewa a sayar da shi.

dan wasan ya taimaka wa Chelsea wadda za ta buga wasan karshe da kungiyar Manchester Metropolis a gasar zakarun Turai, ta lashe Premier biyu da Europa biyu kuma dan kasar Belgium din wanda ya zira kwallo hudu kacal a wasanni 40 da ya buga wa Real Madrid ya ce yana fatan zasu lashe gasar La liga ta bana.

Su ne dai na biyu a jadawalin La Liga, ya yin da wasa hudu ya rage a gama gasar, inda Atletico Madrid ta ke samansu da maki biyu kawai sai kuma kungiyar Barcelona wadda take mataki na uku.

An fara danganta dan wasa Hazard da komawa tsohuwar kungiyar tasa ta Chelsea domin zaman aro na shekara daya sannan kuma ana ganin zai iya komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a ya yinda Real Madrid take son bawa United din shi domin daukar Paul Pogba, dan Faransa.

- Advertisement -