Hasumiyar Wani Tsohon Masallaci Da Ta Yi Saura A Kan Ruwa Bayan Nutsewar Masallaci

0
104

Hasumiyar Wani Tsohon Masallaci Da Ta Yi Saura A Kan Ruwa Bayan Nutsewar Masallaci

Jaridar Day by day Sabah ta bayar da rahoton cewa, a cikin lardin Aghari na kasar Turkiya, wata hasumiyar wani tsohon masallaci da ya nutse a cikin ruwa ta yi saura a kan ruwa, inda har yanzu take tsaye ba tare da ta fadi ba.

Wannan lamarin ya faru ne a kauyen Bash Jawish da ke cikin Lardin Aghari, bayan gina wata babbar madatsar ruwa, wanda hakan ya yi sanadiyyar nutsewar gine-ginen kauyen da dama, da hakan ya hada har da wani tsohon masallaci da ke yankin.

Babbar koramar da ke yankin ce ta cinye gidaje da sauran gine-gine da suka hada har da na masallacin, amma abin mamaki shi ne yadda har yanzu hasumiyar masallacin take tsaye.

Wannan yanki dai yana a Gabashin Kasar Turkiya ne, kuma yanki ne da ake fama da sanyi a lokacin hunturu, inda dusar kankara kan rufe yankin baki daya, wannan korama kuma tana daskarewa ta koma kankara har zuwa karshen lokacin hunturun sanyi.

What's On Your Mind?