Harin ‘Yan Bindiga Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutum 83 A Zamfara

0
145

Harin ‘Yan Bindiga Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutum 83 A Zamfara

Daga Maigari Abdulrahman

Harin ýan bindiga a wasu kauyukan jihar Zamfara ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 83 tare da raunata daruruwa, ciki har da mata da kananan yara.

Mazauna yankunan da abin ya faru, ganau da kuma hukumomi ne su ka tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba a yankunan Gusau, Maradun, Bakura.

Jamiín karamar hukumar Bakura, Aminu Sulaiman ya shaidawa manema labarai mutuwar akalla mutum 30 a Bakura da Maradun. Sai dai ya bayyana cewar, an samu mace-macen ne biyo bayan gwabzawa tsakanin ‘yan sa kai da kuma yan bindigar a kwanaki.

A garin Magami, mazauna garin solar tabbatar da samun gawarwaki 53 da safiyar Alhamis. Inda su ka bayyana cewar, maharan gari-gari su ka bi yayin harin ba tare da wata barazana garesu ba.

Mazauna garin solar kasance cikin fargabar wani harin mahara a yayin da su ke shirin yin salla ga mamatan. Wasu garuruwan fargaba da tsoron wani harin ya jinkirta yin janaízar mamatan a lokacin.

Mazauna garuruwan solar bayyana yanda harin ya kasance, inda su ka ce, a kan mashuna ne ‘yan bindigar su ka kai harin inda suke dauke da manyan bindiga da makamai. A cewar su, da yawan kauyukan mazauna garin solar tashi tuni, solar dawo ne yanzu domin yin noma yayin da maharan su ka kawo hari.

Kauyukan da harin ya afku solar hada da Gora, Rini da Madoti Dankule a karamar hukumar Maradun da Bakura.

Rashin jami’an tsaro a yankin ya sabbaba cigaba da samun hare-hare a yankin, haka kuma cigaban abinda ake fuskanta a tsakanin yan bindigar da ýan sa kai, a cewar mazaunan.

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da hare-haren, ta kuma jajanta wa wa iyalai da yan uwan da abin ya shafa. Haka kuma ta yi alwashin hukunta masu hannu a ciki tare da magance faruwar hakank, kamar yadda kwamishinan labarai a jihar, Ibrahim Dosara ya bayyana a wata sanarwar manema labarai.

What's On Your Mind?