Harin Gujba: Gwamna Buni Ya Yaba Yadda Sojoji Suka Fatattaki Boko Haram

0
29

Harin Gujba: Gwamna Buni Ya Yaba Yadda Sojoji Suka Fatattaki Boko Haram

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba da yadda sojojin Nijeriya su ka fatattaki mayakan Boko Haram a lokacin da su ka kai hari a garin Gujba ranar Asabar.

Buni ya sanar da hakan a takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Daraktan yada labaransa, Mamman Muhammad, wanda ya bayyana cewa ko shakka babu sojojin photo voltaic cancanci yabo a kokarin yaki da matsalar tsaro.

Bugu da kari kuma ya ce a kowane lokaci wannan ita ce babbar manufar jami’an tsaro dangane da arangama da masu tada kayar baya tare da burin canja hali na rashin tsaro wajen samun nasarori kan yan ta’addan.

Har wala yau, Gwamna Buni ya bukaci a kowane yan Nijeriya su ci gaba da yaba wa jami’an tsaron cikakken hadin kai tare da karfafa musu gwiwa ga aikin samar da tsaron a dukan fadin kasa nan.

Moghalu Ya Taya Farfesa Obiozor Murnar Zama Shugaban Koli Ta Ohanaze

Haka zalika kuma, Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa da jama’ar Yobe za su ci gaba wajen bayar da cikakken goyon bayansu ga jami’an tsaro, “Aikin samar da tsaro nauyi ne wanda ya hau kan kowa da kowa ne.”

“Saboda haka gwaamnati za ta ci gaba da bayar cikakken goyon bayan da ya dace domin ganin an samu dawamamen zaman lafiya a wannan jihar.” In ji shi.

A gefe guda kuma ya yi kira ga al’umma da cewa a kowane lokaci su taimaki jami’an wajen sanar dasu dukan wasu take-taken bata-garin da basu gamsu dasu ba a yankunan su domin daukar matakin gaggawa.

A hannu guda, Gwamna Buni ya jajanta wa jama’ar da harin yan ta’addan ya rutsa dasu kana da addu’ar samun sauki ga wadanda su ka samu raunuka ta dalilin harin wanda aka kai shi; kwanaki biyu bayan kai makamancin sa a garin Gaidam, duk a jihar Yobe.

Haka kuma ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta kai wa jama’ar yankin daukin gaggawa domin tallafa wa wadanda harin ya shafa.

Wanda bisa ga wannan ne Buni ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe (SEMA) ta kai wa mutanen Gujba daukin tallafi tare da aikin kiyasta barnar da farmakin ya jawo a garin, don daukar matakin da ya dace.

“Da farko photo voltaic kai wa motar sojoji farmakin kwanton bauna, sannan daga bisani su ka zarce zuwa Gujba. Wanda hakan ya sa mu ka gudu zuwa daji, kuma mun hango hayaki yana tashi,” in ji shi.

What's On Your Mind?