Har Yanzu Muna Da Damar Lashe La liga, Cewar Koeman

0
79

Har Yanzu Muna Da Damar Lashe La liga, Cewar Koeman

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Roland Koeman, ya bayyana cewa har yanzu yana saran kungiyarsa ce zata lashe gasar La liga ta bana da ake kokarin karkarewa a wannan watan na Mayu.

A daren ranar Alhamis ne Barcelona ta barar da damar hawa kan teburin La Liga, bayan da kungiyar kwallon kafa ta Granada ta doke ta da ci 2-1 a filin wasa na Camp Nou dake birnin Barcelona.

Dan wasa kuma kyaftin, Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar kungiyar Granada, bayan da ya yi bani in baka da shi da abokin wasansa, Antoine Griezman, wanda a satin da ya gabata shi ne ya zura wa kungiyar kwallayenta biyu akan kungiyar Billareal.

Barcelona ta barar da damar makin kara zura kwallo a raga, daga baya Darwin Machis ya farke wa Granada a karawar zagaye na biyu, bayan da suka yi hutu sannan saura minti 11 a tashi daga wasan ne Jorge Molina wanda ya shiga fafatawar daga baya ya kara kwallo ta biyu da hakan ya bai wa Granada maki ukun da take bukata.

Da kungiyar Barcelona ta ci wannan karawar da tuni ta hau kan teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid mai maki 73 wadda a yanzu itace ta daya.

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta uku da maki 71 iri daya da na Actual Madrid wadda take ta biyu a teburin da Atletico Madrid ke jan ragama sannan kawo  yanzu sauwa wasa biyar-biyar a karkare kakar La Liga ta bana.

Ranar eight ga watan Mayu za’a fafata tsakanin Barcelona da Atletico Madrid a karawar da ake hangen kila a tantance wadda za ta lashe La Liga na bana a ranar duk da cewa Actual Madrid ma tana bibiyarsu a baya.

What's On Your Mind?