Har Yanzu Lokaci Bai Yi Ba Da Matashi Zai Shugabanci Nijeriya – Rufa’i Daneji

0
145

Har Yanzu Lokaci Bai Yi Ba Da Matashi Zai Shugabanci Nijeriya – Rufa’i Daneji

Da yake an fara hango siyasar zaben shekarar 2023 tun yanzu, magoya bayan ‘yan siyasa photo voltaic fara baje kolin gwanayensu domin kama zuciyar masu jefa kuri’a. Bisa haka ne MOBILIZED9JA A Yau ta samu nasarar zantawa da wani matashi da ke goyan bayan Bola Ahmed Asiwaju Tinubu ya mulki Nijeriya a shekarar 2023. Ga dai yadda hirar ta kasance kamar haka:
Da farko dai masu karatu suna san jin sunanka
Sunana Rufa’i Mustapha Daneji
Chairman/Founder Kano Youths Coalition, Asiwaju 2023
Nationwide Secretary BTG Political Mobement

Mene ne makasudin da ya jawo hankalinka na marawa Asiwaju bayar?
Toh, babban makasudin da ya sa na zabi na marawa Asiwaju baya shi ne, kasancewarsa dan siyasa wanda kullum yake kokarin ganin ya cicciba na kasa izuwa sama, musamman a kokarinsa na karfafa gwiwar matasa don ganin photo voltaic zama nagartattun shugabannin Nijeriya na gobe.
Kana ga wannan bai ci karo da kiraye-kirayen da wasu matasa suke yi ba na ba su damar yin takarar shugabancin kasar nan, wanda har shi ne makasudin fitowar gwamnan Jihar Kogi?
Ka san komai ana bin shi a hankali, har yanzu lokaci bai yi ba da matashi mai irin shekarunmu zai jagoranci Nijeria. Asiwaju mutum ne mai son mu’amala da matasa kuma na tabbata idan ya sami damar kasancewa shugaban kasa zai nada matasa a manyan mukaman gwamnati. Sannan zai yi daga matasa kuma na tabbata a karshe zai mika wa matasa ragamar mulkin Nijeriya don samun ci gaba mai dorewa. Amma mika wa matasa mulki a dai-dai wannan lokacin da Nijeriya ke cikin matsanancin hali bai makata ba. Akwai bukatar samun gogaggen dan siyasa mai shekaru da tarin kwarewa wanda zai sai ta matasan, ya kuma koya musu salon iya tafiyar da tsarin mulki ta yadda za su sami gogewa da kwarewa ta musamman kafin a mika musu madafan iko.
Kana ga matasa za su amince su mara masa baya ganin cewa yana kusa da shugaban kasa Buhari?
Kwarai kuwa. Asiwaju yana da goyan matasa musamman a jihohin Arewa guda 19 da kuma mafi akasarin jihohin Yarbawa da bangare jihohin Igbo.
Amma kwanakin baya ana ta yada jita-jita wai an raba gari tsakanin Asiwaju da kuma shugaban kasa Buhari, mene ne gaskiyar lamari a kan wannan?
Wannan labarin kanzon kurege ne. Makiya ne suke ta kai kawo a tsakani don ganin photo voltaic haifar da matsala a tsakanin Asiwaju da Buhari, amma Alhamdulillahi basu bada kofa ba. Yau ba a yi sati biyu ba matar shugaban kasa ta kaddamar da littafi, wanda Asiwaju shi ne ya kasance babban bako na musamman kuma mai kaddamar wa. Ka ga idan akwai tsamin mu’amala da hakan bai yiwu ba. Saboda haka maganar raba gari babu ita.

Nigeria Youth Investment Fund: Abu uku da suka kamata ku sani kan samun tallafin matasa N75bn

Amma an ce Asiwaju ya rage zuwa fadar shugaban kasa ba kamar yadda yake zuwa ba a baya, mane ne gaskiyar lamarin?
Dabi’arsa ce a haka. Ai tun da aka gama yakin kafa gwamna shi ba ma’abocin zuwa fadar shugaban kasa ba ne, tun da ba shi da ofishi a fadar. Ka san yana da kokarin kiyaye ka’idar tsarin mulki. Shi jagoran jam’iyar APC ne na kasa, ofishinsa ba a billa yake ba. Kuma ga wani abin lura, ko yaransa da ya bayar aka saka a cikin gwamnati baya zuwa wajen su kuma ba ya tsoma baki a al’amuransu na sha’anin gudanar da gwamnati, wannan ne ya sa suke ganin girmansa kuma suke zaune lafiya da juna. Ko ka taba ji ance yana zuwa ofishin mataimakin shugaban kasa ko Fashola da sauran su tun da aka gama yakin kafa gwamnati?
Kasancewar Jihar Kano ita ce ke da yawan kuri’u a yankin Arewa, kana ganin al’umma jihar za su ba shi goyan baya dari bisa dari?
Kwarai, muna kyakkyawan zaton hakan.
Siyasar Jihar Kano ta sha bamban da sauran jihohin kasar nan, ta wata hanya za ku fara kama zukatan mutane jihar?
A yanzu haka muna nan muna aiki tukuru wajen wayar da kan al’umar Jihar Kano, don su fahimci wane ne Asiwaju? Kuma Alhamdulillahi, duk da kokarin bata shi da wasu tsirarun ‘yan adawa suke yi, a yanzu haka akwai ci gaba matuk, domin al’uma suna fahimtar sa kuma suna bamu goyon baya dari bisa dari. In sha Allahu muna sa ran Asiwaju zai sami fiye da kuri’un da Buhari ya samu a zaben shekarar 2023, ba ma a Jihar Kano ba har ma a kasa baki daya.
Kana ga wannan akida na cewa, shi musulmi ne daga yankin Kudu kuma dole ya tsayar da wanda ba musulmi ba a wani yankin ba zai kawo nakasu da tafiyarsa ba?
Wannan ba zai kawo nakasu ba. Tsayar da wanda ba musulmi ba a matsayin mataimaki baya cikin kundin tsarin mulki, saboda haka bana ganin wannan a matsayin wata gagarumar matsala. Kwanan nan el-Rufa’i ya tsaya takara a matsayinsa muslim kuma ya tsayar da mataimakiyarsa muslima a Kaduna, ka ji wani abu ya faru? Duk da dai na san akwai bambamci, amma samun mahimmiyar fahimta kadai kawai ake bukata tsakanin Kudu da Arewa.

Daga karshen, mene ne fatanka a cikin harkokin siyasar kasar nan?
Ina fatan Allah ya bai wa Asiwaju shugabancin Nijeriya. Kuma ina rokon Allah ya ba shi ikon fitar damu matasa da sauran ‘yan kasa kunya. Fatan mu ya samu ci gaban matasa, idan ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara eight ya bamu (matasa) mulki a kuma zauna lafiya.
To Allah ya taimaka malam Rufa’i. Mun gode da bamu lokacinka. Muna fatan idan wani lokaci muka bukaci irin wannan za a ba mu dama.
Ni ma nag ode kwarai malam Yusuf. In sha Allahu a duk lokacin da kuka bukaci hakan zany i kokari.

What's On Your Mind?