Har Yanzu Gwamnatin Biden Na Bin Turbar “Tabbatar Da Moriyar Amurka A Gaban Komai”

- Advertisement -

Har Yanzu Gwamnatin Biden Na Bin Turbar “Tabbatar Da Moriyar Amurka A Gaban Komai”

Daga CRI Hausa

Har yanzu, manufar “tabbatar da moriyar Amurka a gaban komai” da gwamnatin Joe Biden ta kasar Amurka take aiwatarwa, na ci gaba da haifar da wahalhalu sosai ga sauran sassan duniya baki daya.

A da, a fili gwamnatin kasar Amurka, ta rika aiwatar da manufar nuna wariya a fannin samar da allurar rigakafin COVID-19, a yanzu kuma, ta samar da karin kudade a kasuwa kamar yadda take so, domin kokarin ingiza bunkasa tattalin arzikinta. Sakamakon haka, masu fashin baki solar nuna cewa, har yanzu gwamnatin Biden, tana daukar matakan da za su lalata moriyar sauran sassan duniya, domin kokarin tabbatar da moriyar Amurka kadai.

Ko da yake, a kullum shugaban kasar Amurka Joe Biden na jaddada cewa, gwamnatinsa za ta yi watsi da manufar “tabbatar da moriyar Amurka a gaban komai” wadda gwamnatin Donald Trump ta dauka, amma abubuwan da gwamnatinsa ta yi cikin kwanaki 100 ko fiye da suka gabata, solar bayyana yadda suke kama, daidai da fadin Hausawa cewa “Fadi da ba a aikatawa.”
Yanzu haka ba a iya raba allurar rigakafin cutar numfashin COVID-19 ga galibin kasashen duniya kamar yadda ya kamata ba, lamarin da ya zama wata matsala mai tsanani sosai recreation da yaki da annobar, sakamakon manufar nuna wariya da wasu kasashen yammacin duniya suka dauka wajen samar da allurar.

A daya hannun kuma, gwamnatin kasar Amurka ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufar nuna wariya wajen samar da allurar. Bisa alkaluman da wasu hukumomi da kafofin yada labaru na duniya suka fitar, an ce, yawan allurar rigakafin cutar dake hannun kasar Amurka ya kai kimanin biliyan 2.6, wato ya kai kashi 1 cikin hudu na dukkan allurar da aka samar a duk fadin duniya. Yanzu haka kuma, yawan allurar dake cikin dakunan adana kayayyaki ya wuce miliyan 100, kuma solar wuce bukatun da ake da su a cikin gidan kasar Amurka.
Bisa matsin lambar da sauran kasashen duniya suka yi mata, a kwanan baya, gwamnatin Biden ta dauki wasu matakai. Alal misali, ta ce, za ta nemi a yi watsi da ’yancin mallakar fasahar nazari da kuma samar da allurar rigakafin cutar COVID-19. Amma yanzu abun tambayar shi ne, ko dukkan kasashen duniya, da kamfanoni masu mallakar irin wannan ’yanci, ko kungiyoyi masu kula da ’yancin mallakar fasaha za su iya yarda da a yi hakan?
Sannan a ranar 17 ga watan Mayu, gwamnatin Biden ta sake shelanta cewa, daga karshen watan Yuni mai zuwa, kasarsa za ta samar da karin allurar rigakafin cutar miliyan 20 ga sauran sassan duniya.

Amma matsalar a nan ita ce, ko zai cika alkawarinsa? Yanzu haka ana ganin yadda kasashen Sin da Rasha suke samar wa sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa allurar rigakafin cutar kamar yadda ake fata. Amma har yanzu, ba a ga hakikanin matakan da ya kamata kasar Amurka ta dauka ba.

Bugu da kari, yanzu haka dukkanin kasashen duniya na fuskantar hauhawar farashin kaya a kai a kai, sabo da manufar hada hadar kudi da gwamnatin kasar Amurka take aiwatarwa.

Ko da yake gwamnatin kasar Amurka ta aiwatar da manufarta, ta hada hadar kudi domin ingiza bunkasa tattalin arzikinta, amma wannan manufa ta haddasa hauhawar farashin muhimman kayayyaki, ciki har da kayayyakin abinci da ake bukata a kullum a duk fadin duniya fiye da kima.

Dalilin da ya sa aka yi haka shi ne, matakin samar da dalar Amurka fiye da biliyan 1000 a kasuwa, wanda kasar Amurka ta dauka, ya sa masu zuba jari a kasuwar cinikin kayayyaki suna sa ran za su iya samun karin riba. Sakamakon haka, yawan kudin ruwa da bankuna ke sakawa ya karu, ya kuma tsaya wa karfin dalar Amurka sosai a kasuwar cinikin kudade. Babu sauran zabin da za su iya yi, illa magidanta masu karamin kudi da su kan kashe yawancin kudinsu wajen sayen abinci, su sha wahalhalun hauhawar farashin kayan abinci.

Bugu da kari, ba zai yiwu kasar Amurka ta aiwatar da manufar samar da karin kudade a kasuwa a kullum ba. Wato dai idan wata rana hukumar adana kudi ta Amurka, wato FRB ta dauki matakin kara kudin ruwa, tabbas za a goyi bayan dalar Amurka a kasuwa. Sakamakon haka, dole ne kasashe masu tasowa su dauki matakin samar da karin kudin ruwa, domin tinkarar matsin lambar da za su fuskanta, sakamakon fitowar dalar Amurka. Amma matakin kara kudin ruwa zai haifar da illa sosai ga tattalin arzikin da har yanzu ba shi da karfi, sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Sabo da haka, za mu iya gane cewa, ko da yake gwamnatin Biden ta ce, za ta yi watsi da manufar “tabbatar da moriyar Amurka a gaban komai”, amma har yanzu tana ci gaba da aiwatar da ita cikin sauri, ko da yake an shaida ce, wannan manufa kuskure ce kwarai. Sauran sassan duniya ma na ci gaba da shawo kan illoli, da yunwa, da talauci, sakamakon wannan manufar.

A cikin wani jawabin da ya gabatar a watan Fabarairun bana, recreation da manufar diplomasiyyar kasar Amurka, ya shelanta cewa, “Amurka ta dawo”. Amma idan kasar Amurka tana son samu amincewa daga dukkanin duniya gaba daya, dole ne ta yi watsi da manufofin son kai, sannan ta aiwatar da manufofin hadin gwiwar bangarori daban daban. (Sanusi Chen)

- Advertisement -