Zanga-zangar #EndSARS: Har Yanzu Da Sauran Rina A Kaba

0
45

Har Yanzu Da Sauran Rina A Kaba

Daga dukkan alamu har yanzu da sauran rina a kaba akan zangazangar kawo karshen rundunar yan sandan na ta SARS, zanga-zangar kin jinin yan-sandan SARS ta barke ne ta dalilin wani faifan bidiyon da ake zargin jami’an rundunar musamman din da gallaza wa wani matashi a gaban hutal din Wetland Resort da ke Ughelli a jihar Delta.

Yayin da wannan faifan ya karade kafafen sada zumuntar zamani, tun ranar 3 ga Oktoban 2020, wanda ake kallon shi ne kanwa uwar gami tare da ya tayar da tsimin matasan jihar, ta hanyar gudanar da jerin gwanon nuna kin jinin jami’an tsaron.

Ana haka kwatsam, ranar Talatar 8 ga watan Oktoban, wannan zanga-zangar ta rikide zuwa wasu sassan kasar nan, lamarin da ya kara harzuka matasa gudanar da zanga-zangar nuna dole a soke wannan runduna ta SARS; yayin da matasan tare da samun goyon bayan yan rajin kare hakkin bil Adam, rike da kwalaye da hotunan zargin cin zarafi daban-daban wanda jami’an ‘yan sandan ke yi ga yan kasa.

Jerin-gwanon ya ci karo da fushin yan-sandan Nijeriya a wasu jihohin kasar nan, inda su ka yi kokarin tarwatsa matasan da barkonon tsohuwa tare da yin harbi ga masu zanga-zangar lumanar a Abuja da Osun da sauran su, inda hakan ya yi sanadiyar rayuwar Mista Jimoh Isiak a jihar Oyo.

Abin bai tsaya nan ba, ranar Lahadin 11 ga Oktoba, wadannan matasan, photo voltaic gindaya wa gwamnatin tarayya sharudda biyar idan ta na son zanga-zangar ta tsaya, wadanda suka kunshi dole a sako ilahirin wadanda aka kama a lokacin jerin gwanon, kuma a biya diyyar mutanen da yan-sandan suka yi wa kisan gilla.

Bidiyo: Waka Da Ta Fi kowace “Views” A Youtube kaf Kannywood Data Haura fiye Da Miliyan Shidda

Bugu da kari kuma, matasan photo voltaic bukaci a kafa kwamiti mai zaman kansa, cikin kwanaki 10 don gudanar da bincike tare da damke yan-sandan da su ka yi wacan aika-aika. Photo voltaic kuma nemi kafin a tura jami’an SARS wajen aiki dole a yi musu gwajin kwakwalwa, sannan dole gwamnatin tarayya ta rinka biyan yan-sanda isasshen albashin da ya dace.

Hakan ya jawo ala tilas gwamnatin tarayya ta durkusa kasa tare da daukar matakan cika wadancan sharudda, inda kan ka ce me shugaban rundunar yansanda na Nijeriya soke rundunar baki daya. Baya ga sabbin matakai daban- daban da gwamnatin ke dauka, amma abin ya ci tura; zanga-zangar sai kara jan hankin matasan saura jihohi take wanda hakan bai tsaya nan ba, matasan photo voltaic fara jawo hankalin duniya.

Bugu da kari kuma, har yau da nake hada wannan rahoton, zanga-zangar ba ta tsaya ba, bilhasali ma kullum sai ci gaba take tare da kara zakulo wata matsala, kuma akwai fargabar abin ya zarta yadda ake zato. Wanda hakan ya ankarar da masana da manazarta tare da kira ga gwamnatin tarayya ta bi a hankali kar kilu ta ja bau ko kuma wankin hula ya kai dare.

A hannu guda kuma, daya daga cikin tsoron da ake ji shi ne, mafi yawan masu jerin gwanon matasa ne, sannan kama zanga-zangar ta zo a wani yanayi wanda ya yi kusa ya kai talaka zuwa bango. Wanda bisa wannan ne ya jawo matasan ke samun goyon baya tare da kwarin gwiwa, lamarin da idan ba a zurfafa tunani ba abin zai iya daukar sabon salo.

A irin wannan lokaci, dole a dauki matakan hankali da kaffakaffa wajen zuba wa wannan kurar ruwan sanyi, sannan kuma matukar gwamnati ko jami’an tsaro photo voltaic gwada amfani da karfi, hakan yana iya kara harzuka matasan. Saboda gaskiyar magana akwai wahegen gibin kyakkyawar mu’amala tsakanin jami’an tsaro da al’umma, a gefe guda kuma gwamnati tana jan kafa dangane da abinda ya shafi rayuwar matasa ta fuskoki daban-daban.

Mu dauki misalin matsalolin da su ka haifar da zanga-zangar da ta barke a wasu kasashen Tunisiya da Misra a shekarun baya, wadanda su ka yi sanadin tunbuke shugabancin shugaba Zine al-Abidine Ben Ali da Husne Mubarak. Kana da ta baya bayan nan, a kasar Sudan, wanda ta tilasta wa shugaba el-Bashir sauka daga karagar mulkin shi.

Saboda wannan, gwamnati ta kula sosai tare da amfani da kalaman lalama da kawo sauye-sauye kan yadda ake gudanar da tafiyar da mulkin jama’a, kuma ya dace jami’an tsaro su sake damarar kyautata alaka da yan kasa, wanda sai da dan gari a kan ci gari.

What's On Your Mind?