Han Zheng Ya Halarci Taron Kolin Tattara Jari A Kasashen Afrika

- Advertisement -

Han Zheng Ya Halarci Taron Kolin Tattara Jari A Kasashen Afrika

Daga CRI Hausa

Jiya da dare ne, mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng ya halarci taron kolin tattara jari a kasashen Afrika ta kafar bidiyo.

Han ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, kawancen Sin da Afrika na da makoma iri daya.

Tun barkewar cutar COVID-19 a duniya, Sin take namijin kokarin taimakawa Afrika.

Han Zheng ya nuna cewa, yayin da ake kokarin tinkarar wannan annoba tare, abin dake gaban kome shi ne farfadowa da raya Afrika, sport da hakan, Sin ta gabatar da shawarwari hudu, wato na farko nacewa ga alkawarin da aka yi don tallafawa Afrika sassauta matsin da take fama da shi ta fuskar basussuka. Sin tana kokarin tabbatar da shawarwari na G20 don ci gaba da hadin kai da kasashen duniya bisa ka’idar “hadin kai da daukar nauyi baki daya” wajen cika alkawarinsu a fannin rage basusukan da ake bin kasashen Afrika.

Na biyu, nacewa ga hadin kai da cin moriya tare, ta yadda za a farfado da tattalin arzikin Afrika. Sin tana goyon baya hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa da kamfanoni masu zaman kansu da sauransu, da su habaka zuba jari a Afrika na dogon lokaci da inganta karfinsu ta fuskar manyan ababen extra rayuwa, ta yadda za a taimakawa kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa mai dorewa bisa dogaro da kansu.

Na uku, nacewa ga samun bunkasuwa da kiyaye muhalli, da ingiza kwaskwarimarta. Sin tana fatan yin mu’ammala da kasashe daban-daban bisa shirin “Babban ganuwa na Afrika mai kiyaye muhalli”, don rarraba dabaru da fasaha. Na hudu, tsayawa tsayin daka kan taimakawa juna da ingiza rarraba allurar rigakafi bisa daidaito. Sin za ta ci gaba da samarwa Afrika taimako a wannan fanni tare da ingiza sayar da allura ga kasashe daban-daban.
Kasar Faransa ce ta kira wannan taro ta kafar bidiyo da fuska da fuska, inda aka zartas da sanarwar taron koli na tattara jari a Afrika. (Amina Xu)

- Advertisement -