Haduwar Jini (4)

0
84

Haduwar Jini (4)

Daga Kabir Yusuf

([email protected]) 09132880426,

Bayan kwana daya da afkuwar hakan sai Salamatu kawar Lantana ta ziyarce ta har gida. Solar yi doguwar hira,sannan Lantana ta bayyana mata irin son da mijinta yake yi wa Munayya, Salamatu sai ta ce mata:”ai ke ki ka bari har hakan take faruwa mi ya sa ba zaki raba tsakaninsu ta hanyar asiri ki huta kawai ba? “Sai Lanatana ta ce, ni ma na fara tunanin hakan, amma ban san hanyar da zan bi ba”Salamatu sai ta ce, ni nasan wani zazzafan Boka wanda da zaran ya yi aiki to ana samun nasara domin kuwa ana masa lakabi da gobe da nisa. Lantana ta karbi wannan shawarar hakan ya sa a yammacin ranar suka tafi wajen Boka Tanko wanda yake a kauyen Korayal.Isar su ke da wuya ya yi kintacen matsalar da ta kawo su wajen shi.Ya bayyana wa Lanata cewa da ta zo da wuri da matsalar ta ba ta kai haka dadewa ba, amma yanzun ma ba ta baci ba “Ya bayyana mata cewa:”amma fa akwai sharadi mai  girman gaske da idan ta yarda shike nan, idan kuma ba ta yarda ba zai yi mata aiki ba.

Cikin hantsari Salamatu ta ce, kawai ki amince. Sai Boka Tanko yace,sharadin shi ne zan kebe da ke a cikin dakina, daga nan sai in baki maganin matsalar ki”. Lantana ta ji maganar kamar saukar aradu a kanta, amma tun da tana son biyan bukata sai ta amince da hakan. Bayan ya gama biyan bukatarsa da ita,sai ua ba ta wani ruwa a wata jarka sannan ya nemi ta yi wanka da shi rabi sannan ta zuba rabin a hanyar da ta san Munayya da Mahaifinta suna takawa. Solar karba solar koma gida ta kuma aiwatar da hakan. Cikin kankanin lokaci sai kaunar da Mal. Kabir yake nunawa Munayya ta koma kiyayya, darajta ta da ya ke yi ta koma wulakanci, har ya zamanto baya son ya hada ido da ita,hatta idan ta je gaida shi baya amsar gaisuwarta. A haka ta kasance tsawon lokaci a gidan nan ba ta samun abinci da sauran kayan bukatu har sai ta tafi gidan kawarta Jidda da suke makaranta a tare sannan take samun sukuni.

Ita kuwa Lantana bayan ta dawo kawai sai ta fara laulayi alamun ciki duk ya bayyana a gare ta. A sakamakon yadda asirin ya mallake mata  Mal. Kabir tana sanar da shi ba ta da lafiya ko bincike bai yi ba,ya tafi asibiti da ita domin bincikar lafiyarta. Likita ya tabbatar musu cewa tana dauke da ciki. A haka suka dawo gida tana ta tunanin abunda ya wakana tsakaninta da Boka Tanko.

Bayan tsawon lokaci sai Munayya ta shiga wani yanayi mawuyaci tsakaninta da Mahaifinta du a sakamakon asirin da Lanatana ta je wajen Boka ya yi mata.Duk da hakan a duk safiya tana tashi taje ta gaida Mahaifinta Mal Kabir wani lokacin ya amsa wani lokacin yaki amsawa.A haka dai suka dauki tsawon lokaci har ya zuwa lokacin da Lantana ta haifu a yayin da ta samu diya mace aka sa mata Shamsiyya.

AUREN MUNAYYA DA HAIDAR!

Bayan kammala hutun Munayya sai ta koma Makaranta a yayin da ta kammala zangon karshe da ya rage mata.Bayan kimanin watanni uku ta dawo gida.A yayin da Haidar shi kuma tun shekarar da ta wuce ya kammala dugirinsa a kan course din Halayyar dan Adam a Jami’ar FUD-DUTSE.

Watan Jimada Sani ya kama a yayin da aka  fara shirye-shiryen auren Munayya da Haidar.Ta bangaren Mal.Kabir kuwa a sakamakon yawan addu’oinsa sai ya asirin da Lantana da kawarta suka yi ya fara sakin jikinsa har ma ya dawo hayyacinsa.Ya tanadi kayan da Mahaifi yake wa diyarsa dai-dai gwargwadon hali. Haka bangaren su Haidar ma solar kammala shirye-shiryensu na aurar da dansu. Ranar daurin aure ta zo aka yi daurin aure lafiya cikin annashuwa da farin ciki.A yayin da dukkanin bagarorin Munayya da Haidar suka godewa Allah a bisa ni’imar da ya yi musu na aurar da ‘ya’yansu.

BANGAREN LANTANA!

Ita kuma Lantana tun bayan daura auren Munayya sai ta ga alamun sihirin da ta yiwa Mal.Kabir ya warware domin kuwa ya dawo cikin hayyacinsa.

Tun daga wannan lokacin kuma ta shiga cikin kunci matukar a sakamakon aikinta.

Ita kuma diyarsa Shamsiyya tun sadda ta girma ta kai shekara 10 sai aka riga ganin halayyar banza a tattare da ita.Rashin zuwa Makaranta bin gidajen kawaye na cikin ayyukan da ta shahara da su.Shi kuma Mal.Kabir a kullum yana cikin damuwa a sakamakon halayyar da diyarsa take nunawa.Amma kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen yi mata addu’oinin shiriya.

A kullum Mal.Kabir yana kallon irin tarbiyyar da nagartar Munayya wacce ba ta taba aikata wani aiki da ya muzanta shi ba a idon al’umma.Amma kuma sai ga shi yanzu Shamsiyya tana aikata miyagun ayyuka da suke zubar masa da mutunci.

A bangaren ayyukan gida kuwa sam ba ta yin komai  musamman sharar gida,dafa abinci da wanke-wanke.Abunda ta sani kawai shi ne a dafa abinci ta zo ta ci hakan kuwa na bakanta ran Mahaifiyarta Lantana.

Munayya da Haidar kuwa tun bayan da aka daura musu aure rayuwarsu ta karayin inganci.A yayin da giramama juna,tausayin juna,taimakon juna ya lullube rayuwar aurensu.Munayya ta san hakkokin mijinta a kan ta,shi ma Haidar ya san hakkokin matarsa a kan shi.Da zaran Haidar ya fita wajen shagonsa da yake sayar da kayan masrufi,Munayya take kimtsa gidan tattare da mai da shi abun sha’awa.Da misalin karfe daya Haidar yake komawa gida domin ya ci abincin rana.Tun kafin isar sa gidan zai kira ta a waya ya bayyana mata cewa ya kusan zuwa gidan a yayinn da take kimtsa abinci da tanadar masa abunda yake bukata.Irin tarairaya da kulawar da Haidar yake samu a wajen Munayya ya sa shi kara gaskata Hadisan Manzon Allah (s) da yake ce wa,hakika Duniya muhallin jin dadi ce,amma mafi alkairin jin dadin ta mace ta gari.”

Mal.Kabir yakan kaiwa Munayya ziyara duk bayan wata guda domin bincikar halin da take ciki.

Lantana abun Duniya ya ishe ta a sakamakon kunci da halayyar da diyarta Shamsiyya take nunawa.Kwatsam sai ta fara zargin anya ba alhakin Munayya ba ne ba ya bita kuwa?Wannan tunani ya dade yana damunta a ranta.Amma sai ta ci gaba da istigfari ga Allah sai kuma tunanin ce wa hakika Allah ba ya yafe laifin da ke tsakanin bayi har sai idan mutanen ne suka yafewa kawunansu.

Bayan kimanin wata uku sai sakamakon jarabawar su Munayya ya fito a yayin da ta samu sakamako mai kyau.

A dai-dai lokacin ne kuma Gwamnatin Jihar Jigawa take neman ma’aikata lafiya wanda Munayya ta samu kanta cikin wadanda aka dauka.Bayan kammala tantancewa ne aka kai Munayya bangaren kula da magungunan asibitin garin Roni da ke Jigawa state a matsayin shugaba mai kula wannan bangaren.Munayya ta yi farin ciki da aikin da ta samu a yayin da ta godewa Allah a bisa ni’imar da ya bata.Mal.Kabir shi ma ya yi godiya ga Allah a bisa ni’imar samun aikin da diyarshi ta yi.

NADAMAR LANTANA

A sakamakon bakin cikin halayyar da Shamsiyya take nunawa Mahaifiyarta Lana

tana,hakan ya sabbaba mata matsananciyar damuwar da ta kai ta ga kamuwa da hawan jini.

A daya daga cikin ranaku ne Lantana ta nemi Munayya da zo domin su tattauana wata muhimmiyar magana tattare da Mahaifinta,hakan kuwa aka yi Munayya ta nemi izinin mijinta Haidar ta ziyarci gidan Mahaifinta domin ta ji zaman da Lantana ta ce za su yi a tsakanin Mal.Kabir da ita.A sadda aka zo zaman ne sai Lantana ta kwashe dukkanin labarin zuwanta wajen Boka da ire-iren makirce-makircen da kulla da yadda Boka ya kebe da ita har ta samu juna-biyu ta  bayyanawa Mal.Kabir.A nan ne ya sadda kansa kasa saboda bakin ciki da takaici sannan ya numfasa ya ce,”lallai kin cuce ni sosai,kuma dama a jikina ina jin an ya Shamsiyya jini na ce kuwa?Amma sai ga shi yanzu Allah ya matsi bakinki kin bayyana hakikanin Shamsiyya da asalinta don haka ni bazan iya ci gaba da zama da ke ba a nan ne Mal.Kabir ya sake ta.

A yayin da Munayya ta buda baki tace,ni na yafe miki cutarwar da kika yi mini,amma ki sa ni kin cutar da ni matuka.

Mal. Kabir ya rarrashi Munayya a a yayin da ya bayyana mata ce wa,ta yi hakuri da abunda ya yi mata,sannan ya bayyana mata ce wa,dama alhaki kwikwiyo ne mai shi yake bi.Ga shi ki ga karshen Lantana da irin cutarwar da ta yi miki.”Munayya ta ce,”ba komai Abbana Allah ya yafe mana kura-kuranmu gaba daya.”

 

 

What's On Your Mind?