Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki

0
21

A wani yunkuri na bazata, wata hadimar Gwamnan jihar Ebonyi tayi murabus daga gwamnatin.

Hadimar wacce kafin murabus dinta take a matsayin babbar mai bayar da shawara ga gwamnan kan ci gaban kasuwanci ta bayyana dalilinta na ficewa daga gwamnatin.

A wasikar murabus dinta mai kwanan wata Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, wanda Legit.ng ta gano, Deaconness Udeakaji ta bayyana cewa murabus din nata ya zama dole domin tsiratar da aurenta.

Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki

Ta riki cewa a lokacin da take yiwa jihar hidima, ta yi biyayya ga gwamnatin dari bisa dari, amma a yanzu ana magana ne a kan iyalinta.

Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai
Wasikar da ta aikewa Gwamna Umahi ya zo kamar haka:

“Ina mika godiya ga mai girma Gwamna, matarsa da ahlin Umahi a kan damar da suka bani don yin aiki a wannan gwamnatin.

“Nagode sosai yallabai. Na ajiye aiki ne saboda matsalolin gidana. Na yi biyayya ga wannan gwamnati dari bisa dari amma gidana na tarwatsewa.

“Littafin Injila ya ce , ‘mace ta zamo mai sadaukarwa ga mijinta’. A matsayina na mai hidima, ya zama dole na koma na kuma yi nazarin littafina mai tsarki sosai. Domin biyayya ga wannan littafin mai tsarki, na yanke shawarar yin murabus da ceto aurena.

“Ina matukar godiya a kan dukkan abubuwan da kuka yi mun. Ni ba butulu bace kuma ba zan taba zama butulu ba. Dan Allah kuyi hakuri dani saboda yarana. Ina maka fatan alkhairi a harkokin siyasarka na gaba. Nagode, ya mai girma kuma ka ci gaba da kasancewa cikin aminci.”

A wani labari na daban, manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) solar shawarci Gwamna Yahaya Bello da Gwamna David Umahi a matsayin mafi kyawun ‘yan siyasa da zasu mulki Najeriya a 2023.

Shawarwarin solar fito ne daga kakakin majalisar dokokin Kogi, Mathew Kolawole, da takwaransa na majalisar Ebonyi, Francis Nwifuru.

Duk mutanen biyu a wajen taron siyasa a jihar Ebonyi solar yi ikirarin cewa Bello da Umahi suna da kwarewar da ake bukata don shugabancin kasar.

What's On Your Mind?