Gyara Lantarkin Da Karamar Hukumar Gumi Ta Yi Zai Bunkasa Arzikin Yankin

0
78

Gyara Lantarkin Da Karamar Hukumar Gumi Ta Yi Zai Bunkasa Arzikin Yankin

Daga Husssaini Yero,

Al’ummar karamar hukumar Gumi da ke jihar Zamfara,solar yabawa shugaban karamar hukumar, Honarabul Abubakar Shehu Daki Takwas saboda dawo da wutar lantarki a cikin garin Gumi, bayan an shafe wata takwas babu ita.

Mazauna garin solar nuna jin dadinsu bisa wannan aiki da shugabanin karamar hukumar ya yi, na sake sa taransifoma mai karfin 2.5 KBA.

Sufiyanu Dan-Iya Gummi, Mataimakin shugaban kungiyar (HAYAS) ya bayyana cewa, saboda rashin wutar lantarki a manyan yankunan karamar hukumar, an jefa kananan kamfanoni da matsakaitan masana’antu cikin mawuyacin hali.

Mataimakin shugaban kungiyar, ya kara da cewa,solar bi duk hanyoyin da suka kamata su bi don magance matsalar wutar lantarki abin ya ci turo,kuma ya jawo asarar kudaden shigar karamar hukumar da jiha da ma kasa baki daya.

Shi ma a nasa jawabin, Kwamared Akilu Adamu, Sarkin yakin Baraden Gumi, ya ce, shugaban karamar hukumar ya cancanci yabo da kuma babbar kyauta ga matasan yankin za su shirya, a wani mataki na nuna girmamawa da jinjinawa ga shugaban.

A kan haka ne, muke kira ga manyanmu da masu mukaman siyasa da masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wannan kokarin da shugaban karamar hukumar ya yi wajan kawo ci gaban al’ummar Gumi da kewaye.

What's On Your Mind?