Gwamnonin Kudu 17 Sun Yanke Shawarar Soke Kiwon-sake A Jihohinsu

- Advertisement -

Gwamnonin Kudu 17 Sun Yanke Shawarar Soke Kiwon-sake A Jihohinsu

Daga Abubakar Abba,

A ranar Talatar da ta gabata ce, gwkmnonin jihohin Kudu su 17 suka gudanar da taronsu a Asaba, babban birinin Jihar Delta, inda suka yanke shawarar soke yin kiwon shanu a fili a Jihohinsu.

In za a iya tunawa, an jima a jihohin ana kai ruwa rana a tsakanin wasu al’umomin jihar da Fulani Makiyaya da suke yin kaura zuwa jihohin domin yin kiwo, inda hakan ya janyo sace-sace da fadace-fadacen da suka janyo asarar rayukan jama’a da kuma barnata dukiyoyin miliyoyin Naira.

Bugu da kari, wasu daga cikin Fulani Makiayan, an zarge su da aikata manyan laifukka da suka hada da, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma hallaka jama’a.

A taron da aka gabatar, cikin gwamnonin Kudancin 17, 15 solar halarci zaman, wadanda suka hada da, na Delta Ifeanyi Okowa, a Ekiti Kayode Fayemi Nyesom Wike na Ribas, Godwin Obaseki na Edo, Dapo Abiodun na gun, Seyi Makinde na Oyo sai kuma na Legas Babajide Sanwo-Olu.

Sauran su ne, Douye Diri na Bayelsa, Okezie Ikpeazu na Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Rotimi Akeredolu na Ondo, Dabid Umah na Ebonyi sai kuma Willie Obiano na Anambra.

Gwamnonin Jihohin Akwa Ibom da na mataimakansu ne suka wakilce su, inda gwamnonin Jihohin Osun da na Ribas, ba su halarci taron ba .

- Advertisement -