Gwamnonin Arewa: Gwamnatin Kaduna Da Kungiyar Kwadago Ku Mayar Da Wuka Cikin Kube

- Advertisement -

Gwamnonin Arewa: Gwamnatin Kaduna Da Kungiyar Kwadago Ku Mayar Da Wuka Cikin Kube

Kungiyar gwamnonin Arewa solar yi kira da a kai zuciya nesa tare da hawa teburin tattaunawa domin magance sabanin da aka samu tsakanin gwamnatin Jihar Kaduna da kuma kungiyar kwadago, sakamakon korar ma’aikata da gwamnatin jihar take yi.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong shi ya bayyana hakan, inda ya ce kungiyar ta damu matukar da yajin aikin da ake yi a jihar da kuma yadda al’umma jihar suka fada cikin wani hali.

Gwamnonin Arewan solar bukaci a sasanta rikici ta hanyar hawa teburin tattaunawa wanda shi ne hanyar da ya fi dacewa wajen sasanta sabani, domin gudun kar rikicin ya yi kamari ta yadda zai yi wahalar sasantawa.

Ya bayyana cewa, ana iya sasantawa ne kadai lokacin da dukkan bangarorin guda biyu suka amince da bin doka da sharrudan da aka gindaya tare da mayar da wuka cikin kube domin gudun kara hargitsi lamarin wanda zai iya kawo firgici a cikin jihar.

Haka kuma kungiyar gwamnonin Arewan solar bukaci shugabannin kungiyar gwadugo ta samu masu tsaro a kan ‘yan daban da ke kokarin tarwatsa zanga-zanga wanda suke son yin amfani da lamarin wajen barnatar da rayukan mutane da kuma dokiyoyinsu. Ta kuma bukaci jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen tabbatar da doka da oda da kare rayukan mutane a cikin jihar.

- Advertisement -