Gwamnatin Tarayya Za Ta Kawo Karshen Matsalolin Safarar Man Fetur

0
43

Gwamnatin tarayya da nuna damuwarta da karuwar tsarin tankokin man fetur a fadin kasar nan. Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a yanzu haka tana gyara titunan jiragen kasa da ke cikin kasar nan, domin samar da wani tsabi wajen safarar man fetur a fadin kasar nan. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana kokarin magance hadarrukan da ake samu musamman ma na tankokin man fetur.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kawo Karshen Matsalolin Safarar Man Fetur

karamar ministar sufuri, Sanata Gbemisola Saraki, ita ta bayyana hakan lokacin da take jawabi a wajen taron karawa juna sani wanda kun giyar manyan ‘yan kasuwan a Nijeriya (MOMAN) mai suka shirya tare da hadin gwiwar kungiyar sufuri ta kasa wanda ya gudana a Abuja. Ministar wacce ta samu wakilcin mataimakiyar darakto ministar, Misis Oniremi Joke ta bayyana cewa, gwamnati tana kokarin samar da wani tsari wanda zai kula da tankoki a kan babban hanya. Ta kara da cewa, daya daga cikin wadannan tsari dai shi ne, samar da tashoshin tanka.

Da take yaba wa kungiyoyyin sport da gudanar da taron karawa juna sani a kan yadda za a magance matsalolin sufuri, ministar ta bayyana cewa, kungiyoyin ba su makara ba wajen shirya wannan taro sakamakon hadararrukan da ake samu na tanka a fadin kasar nan wanda ke lakume rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu. Ta bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya damu matuka da yadda ake kara samun hadararruka a cikin kasar nan.

“Kamar yadda muka sani, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, tana gudanar da kokari wajen magance matsalolin sufuri a cikin kasar nan, domin ceto rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu, wannan ne ya sa gwamnati take kokarin gyarn hanyoyi da gina sababbi a cikin kasar nan.

KUKARANTA: Gwamnati Za Ta Fara Yi Wa Talakawa Rijistar Tallafin Korona

“Haka kuma, domin saukaka wa hanyoyin tarayya, gwamnatin tarayya tana kokarin gyara titunan jirgin kasa tare da zuba jari mai yawa a harkokin sufuri ta jiragen kasa.

“Domin haka, canza tsohon tsarin sha’anin tankoki zuwa na zamani ya danganta da kayayyakin aiki da na’urori da aka samu daga sufurin man fetur wajen kawo zabi ga kungiyar masu sufuri ta kasa da sauran kungiyoyi.”
A nasa jawabin, shugaban kungiyar MOMAN, Adetunji Oyebanji, ya bayyana cewa, kungiyoyin su hada kai wajen inganta kariya a cikin harkokin sufuri a bangaren mai.

Ya bayyana cewa, kungiyoyin MOMAN da NARTO photo voltaic gudanar da wannan taro ne domin tattaunawa wajen samun mafita ga harkokin sufuri na tankokin mai a cikin kasar nan, inda za a samu kariya da maganci duk wani matsalolin da ka iya tasowa nan gaba.

“Wannan taro bai bayar da damar dukkan daukan matakai na kawo sauyi tun daga kan masu bayar da ayyukan da cibiyoyin kudade da masu amfani da man fetur, inda za a samar da wani tsari a kan tankokin mai tare da kafa wani kwamiti da zai gyara harkokin kasuwanci,” in ji shi.

Ya kara jadda cewa, akwai bukatar samun wani tsari a cikin harkokin sufuri a kasar nan, a duk Duniya an san da cewa ana yin sufurin man fetur ne ta bututun mai da ta jiragen ruwa ko kuma ta hanya.

Sufurin mai ta bututu ya fi dace idan a ka kwatanta da ta ruwa ko ta hanya. An fara amfani da tsarin bututun mai tun a farkon shekarar 1990 a Nijeriya, amma a yanzu an yi watsi da sufurin mai ta bututu a na yi safararsa ta kasa a yau a Nijeriya.”

A nasa bangaren, shugaban kungiyar NARTO, Alhaji Yusuf Othman, ya bukaci gwamnati da ta samar da wata mafita a gare su ta yadda fannin zai ci gaba da bunkasa.

What's On Your Mind?