Gwamnatin Tarayya tayi amai ta lashe, ta dawo da rajistar SIM da ta dakatar

0
15

Yanzu nan mu ke ji daga This Day cewa hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa ta dauki sabon mataki sport da rajistar layin wayoyi.

Gwamnatin tarayya ta bada sanarwa cewa an dakatar da maganar daina yin rajistar sababbin layi da tusa rajistar tsofaffin layukan wayoyi a Najeriya.

Legit.ng ta fahimci wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban jami’in hulda da jama’a na hukumar NCC ta kasa, Mista Ikechukwu Adinde.

Ikechukwu Adinde ya fitar da jawabi a ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020 a madadin NCC.

Gwamnatin Tarayya tayi amai ta lashe, ta dawo da rajistar SIM da ta dakatar

Adinde ya bayyana cewa akwai sharadi kafin ayi wa mutum rajistar layin wayarsa, dole kuwa ya zama mutum ya na da lambar NIN ta zama ‘dan kasa.

Darektan yada labaran ya ce NCC ta dauki wannan mataki ne domin karasa cin moriyar nasarorin da gwamnati ta samu wajen rajistan layin waya.

Gwamna Uzodinma ya na kashewa APC kasuwa a Imo inji Hadimin Okorocha

Wannan ita ce sanarwar karshe da ta fito daga bakin hukumar NCC a shekarar 2020, yayin da ake bikin murnar shiga sabuwar shekara a Najeriya da Duniya.

Kungiyar ALTON ta masu rajistar layin waya ta ji tausayin wadanda su ka shiga matsi a sanadiyyar wannan mataki da gwamnati ta dauka a da.

Gwamnatin Tarayya tayi amai ta lashe, ta dawo da rajistar SIM da ta dakatar

A dalilin haka an hana rajistar duk wani sabon layi, sannan masu neman tasa rajistarsu ba su samu damar yi ba, hakan ya toshewa wasu hanyar samu.

A shafinta na Twitter, hukumar NCC ta cigaba da yin kira ga mutane su yi rajistar lambar NIN. Wannan ya zo ne a sakon barka da shiga sabuwar shekara.

A gefe guda kuma kun ji cewa za a iya rufe layin wayoyin mutane kusan miliyan 162 saboda rajistar NIN da Gwamnatin tarayya ta wajabtawa jama’a.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce dole a hada kowane layi da lambar NIN din mai ita.

Amma masu nazari su na ganin cewa zai yi wahala a iya yi wa miliyoyin mutanen da ake da su a Najeriya wannan aiki a cikin ‘yan kwanakin da aka bada.

What's On Your Mind?