Gwamnatin Tarayya Ta Saka Dokar Kulle Ta Korona Karo Na 4

- Advertisement -

Gwamnatin Tarayya Ta Saka Dokar Kulle Ta Korona Karo Na 4

Gwamnatin tarayya ta sake dawo da dokar takaita fita a duk fadin kasa daga 12 na dare zuwa 4 na asuba domin dakile yaduwar annobar korona.

Mukhtar Mohammed, manajan kula da yaduwar cuta na kasa ne ya sanar da hakan yayin jawabin da kwamitin shugaban kasa kan korona ta yi a Abuja.

Ya kuma ce daga ranar Talata za a rufe wuraren casu na dare, wuraren motsa jiki wato health club da sauran wuraren cinkoson mutane har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ya ce an bada umurnin rage adadin mutanen da ke hallartar wuraren ibadah da kashi 50 cikin 100 yayin da za a cigaba da yin sauran taro da harkoki na gwamnati ta hanyar amfani da fasahar bidiyo na intanet.

Ya ce za a takaita duk wani taron mutane zuwa mutum 50 a kowane lokaci. Ba za a bari mutane su shiga hukumomin gwamnati ba har sai suka saka takunkumin fuska.

- Advertisement -