Gwamnatin Tarayya Ta Raba Gidan Sauro Miliyan 145 A Shekara Shida

0
17

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta raba akalla gidan sauro guda miliyan 145 a Jihohin kasar nan 33 a cikin shekaru shida da suka gabata.

Gwamnatin ta yi nu ni da cewa, duk da cewar ba a iya cimma kudurin kawar da cutar ta cizon sauro kwata-kwata ba, amma dai an samu raguwar masu kamuwa da cutar ta Maleriya a sanadiyar cizon sauro din daga kashi 42 a shekarar 2010 zuwa kashi 27 a shekarar 2015 da kuma kashi 23 a shekarar 2018 a bisa kididdigar hukumar lafiya kan cutar ta Maleriya na shekarar 2018.

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Gidan Sauro Miliyan 145 A Shekara Shida

Babban shugaban hukumar da ke fafutukar kawar da cutar ta Maleriya a kasar nan, Dakta Audu Mohammed, wanda ya bayyana hakan a Abuja, a lokacin da yake bayani a kan inda aka kai a yakin da ake yi da cutar ta Maleriya na shekarar 2014 zuwa 2020, wanda ake gab da karkare shi ya zuwa karshen wannan shekarar, ya yi nu ni da cewa an rarraba gidajen sauron guda miliyan 130.42 a aikin rarraba gidan sauron da ake yi, sannan kuma an rabar da sama da miliyan 16.3 a tsarin nan na maimaitawa a wasu sassan da aka rabar da shi tun da farko.

Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse

Audu ya yi la’akari da cewa tabbas an samu kari a kan yawan masu amfani da gidan sauron a sassa daban-daban na kasar nan. ya ce yawan mata masu cikin da suke kwanciya a karkashin gidan sauron ya kara matuka daga kashi 17 a shekarar 2013 zuwa kashi 49 a shekarar 2015 sannan adadin na su ya sake karuwa zuwa kashi 58 a shekarar 2018. Hakanan yawan yaran da suke kasa da shekaru biyar da haihuwa masu kwanciya a karkashin gidan sauron shi ma ya karu daga kashi 16 a shekarar 2013 zuwa kashi 44 a shekarar 2015 da kuma kashi 52 a shekarar 2018.

What's On Your Mind?