Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Bude Makarantu

0
152

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ba da umarnin sake bude dukkan makarantun a ranar 12 ga watan Oktoba bayan watanni shida da rufewa sakamakon barkewar cutar Korona.

Adamu wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani jawabi a Abuja, ya ce bayan neman shawarwarin kwamitin Shugaban kasa kan Dakile cutar Korona, “Mun yanke shawarar cewa duk Kwalejojinmu na fadin tarayya guda 104 su sake bude makarantun a ranar 12 ga Oktoba, 2020.”

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Bude Makarantu

“Makarantu na gwamnatin Jihohi da masu zaman kansu za su tsara hanyoyin yadda za su bude makarantun dake karkashinsu,” in ji shi.

“Bada umarnin kulle makarantun da farko, wannan hukunci ne mai zafi amma ya zama dole, hankalin gwamnati bai kwanta ba tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki da bin ka’idoji kan yadda za’a sake sabon shirin bude makarantun” in ji shi.

Yan Siyasa Ne Kan Gaba Wurin Lalata Tarbiyyar Matasa, Inji Janar Abdulsalam

“Na yi farin cikin bayar da rahoton cewa duk kwalejojinmu na tarayya 104 da su koma makarantunsu, ba a sami dalibi ko guda daya da ya kamu da cutar korona ba kawo yanzu. Wadanda muka killace a wasu makarantun ba su da yawa. Abin farin ciki ne ce wa gaba daya, ba a samu asarar rai ko daya ba a tsakanin daliban da suka fito bayan killacesu ” inji shi.

What's On Your Mind?