Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Fitar Da Biliyan N1.8 Don Kafa Cibiyoyin Gyaran Mota

0
90

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da tsabar Naira biliyan 1.8 domin sayowa da kafa wasu cibiyoyin gyaran motoci a sassan kasar nan guda shida.

Ministan masana’antu da harkokin kasuwanci, Otunba Adeniyi Adebayo , ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yin jawabi ga manema labarai a Abuja, ya bayyana cewa, majalisar zartaswa ta kasa ta amince da fitar da tsabar wadannan kudade naira biliyan 1.8 domin sayowa da kuma kafa wadannan cibiyoyin.

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Fitar Da Biliyan N1.8 Don Kafa Cibiyoyin Gyaran Mota

A cewar Minista Adebayo, za a kashe kudaden ne a wajen siyowa da kuma kafa wadannan cibiyoyin na gyaran motoci a wasu wurare na musamman a sassan kasar nan guda shida.

Kudaden a cewarsa, za a yi amfani da su ne a wajen fara aiwatar da shirin a sassa uku.
A cewar Ministan, shirin wanda yake da alaka da irin motocin da ake kerawa a sassan Duniya a irin wannan zamanin, “Akwai bukatar mu kafa cibiyoyin horaswa da za su horas da makanikanmu da sauran matasanmu a kan yanda za su rika gyaran motocin.

Bidiyo: Labarin Wani Sufi Dan Damfara: Asirin Wani Shehun Darika Ya Tonu – Sheikh Albani Zaria

Shi ma da yake na shi jawabin, babban daraktan hukumar shirin na NADDC, Jelani Aliyu, ya bayar da tabbacin cewa cibiyoyin gyaran motocin bakwai da ake da nufin kafawa za su koyar da matasanmu, su samar kuma da karin ayyukan yi wanda ya dace da shirin gwamnati na dauke ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga cikin kangin talauci.

Jelani ya ce wuraren uku da a yanzun haka ake kan aikin gina su su ne na Jihohin, Sakkwato, Ondo da Imo, za kuma a wadata su da isassun kayayyakin aiki da kuma samar masu da kwararrun ma’aikatan da suka kamata, wadanda za su iya duba kowace irin mota ce su gyara ta su kuma kula da ita yanda ya kamata.

What's On Your Mind?