Gwamnatin Katsina ta tura Karnuka gadin makarantun jihar

0
73

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da tura karkuna gadin makarantun kwanan jihar domin taimakawa jami'ar tsaro wajen dakile yan bindiga masu garkuwa da mutane. Kwamishanan ilimin jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawaran haka ne domin karfafa matakan tsaro a makarantun kwanan jihar, rahoton TheNation. Yace:

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da tura karkuna gadin makarantun kwanan jihar domin taimakawa jami’ar tsaro wajen dakile yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kwamishanan ilimin jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawaran haka ne domin karfafa matakan tsaro a makarantun kwanan jihar, rahoton TheNation.

Yace: “An bamu shawaran tura karkuna kowace makaranta saboda suna da horaswa na gano wani mai yunkurin kutse fiye da dan Adam.”

“Wadannan karnukan idan aka tura su, zasu ankarar da dalibai da sauran jami’an tsaro idan wasu yan bindiga na kokarin zuwa.”

“Jami’an tsaro ne suke bada wannan shawara kuma mun yanke shawaran gaggauta amfani da shi saboda halin rashin tsaron da muke ciki.”

“Ko ofishohin yan sanda da gidajen masu kudi akwai karnuka domin tabbatar da tsaro.”

Gwamna Bello Masari ya ce gwamnatinsa ta karfafa matakan tsaro a makarantun kwana kafin sake bude su.

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Bude Makarantu

Zaku tuna cewa a bara yan bindiga suka dira makarantar sakandaren Kankara, inda sukayi awongaba da dalibai 342.

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Katsina ta umarci ɗalibai mata dake yin makarantun kwana a faɗin jihar da su koma makarantun dake kusa da su daga ranar Laraba 24 ga watan Maris.

Kuma gwamnatin ta bada umarnin buɗe wasu makarantun guda biyar dake jihar daga ranar Litinin 28 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Makarantun da umarnin ya shafa solar haɗa da; makarantar sakandiren gwamnati dake Malumfashi (Unity), SUNCAIS Katsina, Makarantar mata ta gwamnati dake Dutsin-Tsafe, makarantar sakandiren mata Dutsinma, makarantar kurame dake Malumfashi, da kuma makarantar makafi Katsina.

What's On Your Mind?