Gwamnatin Kano Ta Umarci Dukkan Ma’aikatanta Su Koma Bakin Aiki

0
46

Gwamnatin Kano Ta Umarci Dukkan Ma’aikatanta Su Koma Bakin Aiki

Daga Sulaiman Ibrahim

 

Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan ma’aikatanta da su dawo bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da yafitar a jiya Laraba.

Ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba da wannan umarnin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na mako-mako da ake gudanarwa a Fadar Afirka, dake gidan Gwamnati, Kano.

Malam Garba ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan nasarorin da aka samu a yaki da cutar ta COVID-19 a cikin jihar a cikin watanni uku da suka gabata.

Kano ta sake samun sabbin mutane 6 da suka kamu da cutar ta COVID-19 a ranar Laraba, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC).

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, sakatarorin dindindin da shugabannin hukumomi, an umarce su dasu tabbatar ana bin ka’idoji da dokokin gwamnati na yaki cutar COVID-19 a wuraren ayyukansu.

Ma’aikatan na jihar, solar kasance a gida tun ranar 18 ga watan Janairu, sakamakon bullar cutar.

What's On Your Mind?