Gwamnatin Bauchi Ta Bayyana Kudurin Inganta Harkar Ilimi A Jihar

0
97

Gwamnatin Bauchi Ta Bayyana Kudurin Inganta Harkar Ilimi A Jihar

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya jaddada kudurin gwamnatinsa na bunkasa fannin ilimi da ciyar da shi gaba a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a yayin bukin kaddamar da bayar da kayyayakin karatu ga cibiyar inganta karatu a jihar wato BESDA.

Ya bayyana cewar, gwamnatinsa ta samar da tsare-tsare masu dinbin yawa na ganin an inganta harkar ilimi a jihar, “Gwamnatinmu ta samu gagarumar nasararori wurin habbaka harkar ilimi, kuma a shirye muke domin kara bada gudunmawa da yin abinda ya wuce hakan ma,” in ji gwamnan.

Haka kuma, gwamnan ya godewa gwamnatin tarayya akan tallafin da ta baiwa jihar ta hannun shirye-shiryen UBE. A cewar sa, jiharsa ta anfana da tallafin kayayyakin karatu da yakai kimamin miliyan 900.

“Inganta cibiyoyin karatu tare da samar da kyakkyawan yanayin karatu ne babban dalilin da ya sa aka sawo wadannan kayayyakin,” in ji gwamnan.

A nasa jawabin, shugaban hukumar ilimi ta UBEC a jihar, Mista Abubakar Sirimbi, ya yi kira ga gwamnatinn jihar da ta kara adadin malamai a jihar ta hanyar daukar aiki, yin hakan, a cewar sa, zai kara inganta harkar ilimi da koyarwa a jihar.
Shugaban ya koka da karancin malamai, inda ya bayyana cewar tun 2015 ba a sake daukar malamai a jihar ba.

“A kullum ana samun masu barin aiki, ko ta dalilin ritaya, mutuwa ko aje aiki, saboda haka akwai gibi sosai. Wannan gwamnatin ta yi kokori sosai kan harkar ilimi, sai dai, har yanzu akwai wasu abubuwan da suna bukatar karin kulawa,” in ji shugaban na UBEC.

Ya ci gaba da cewa, “akwai bukatar dawo da tsohon shirin gwamnati kan ilimi domin inganta harkar ilimi a kauyuka da karkara.”

Da yake cigaba, shugaban ya koka matuka kan halin da wasu makarantun su ke ciki, inda ya ce har zuwa yau, firamri din Wunti da Shawanka basada ingantaccen muhallin karatu. Ya yi kira ga gwamnati akan haka, yana mai cewa, “wadannan makarantun suna daga cikin tsaofaffin furamari na farko-farko a Bauchi, ya kamata a samar masu da muhalli da gini na dindin din domin cigaba da aiki.”

What's On Your Mind?