Gwamnati za tayi zama na musamman a kan maganar komawa aji bayan kamarin COVID-19

0
37

A ranar Litinin, 11 ga watan Junairu, 2020, gwamnatin tarayya tace za ta duba maganar bude makarantu da ta sa cewa za ayi a ranar 1 ga watan nan.

Gwamnatin kasar ta ce hakan ya zama dole ne a sakamakon cutar COVID-19 da ta dawo da karfinta.

Jaridar Punch ta ce ai girma Ministan ilmi na kasa, Malam Adamu Adamu, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida jiya a birnin Abuja.

Yace: “Bakin alkalami bai bushe sport da batun bude makarantu a ranar 18 ga watan Junairu ba. Lokacin da muka sa wannan rana, muna harin abin da za mu yi aiki da shi ne kawai.”

Gwamnati za tayi zama na musamman a kan maganar komawa aji bayan kamarin COVID-19

Ministan ya ce suna burin cinma wannan matsayi da suka dauka, amma a daidai lokacin ana kuma duba halin da kasa ta ke ciki.

“Ko a ranar Litinin (wajen taron PTF), mun duba yadda alkaluma suke tashi, kuma mun yi maganar duba wannan rana da aka sa.” Inji Ministan.

Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da ‘yan bindiga a Katsina

Adamu Adamu ya tabbatar da cewa a ranar Talata ne ma’aikatarsa za ta zauna a kan maganar ranar komawa karatun domin a dauki matsaya.

Ganin yadda ake samun karuwar masu dauke da Coronavirs, Adamu Adamu ya nuna akwai matsala sport da ranar da suka sa da nufin dalibai su koma aji.

Yau ne ake tunani ma’aikatar ilmi za ta bayyana ranar da za a koma shiga aji bayan an rufe makarantun saboda takaita yaduwar cutar COVID-19.

Dazu kun ji cewa NCDC ta fito ta ja-kunnen Jama’a bayan COVID-19 ta harbi mutane 100, 000.

Shugaban NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu ya ce cutar Coronavirus ta kai intaha a yanzu, ana gab da cike gadajen asibiti da masu jinya a Najeriya.

Dr. Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka ne a wasu bayanai da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin bayan masu cutar solar haura mutane 100, 000.

What's On Your Mind?