Gwamnati Za Ta Fara Yi Wa Talakawa Rijistar Tallafin Korona

1
187

Gwamnatin tarayya a karkashin hukumar kare harkokin zamantakewa za ta fara yi wa talakawan Nijeriya da mabukata rijista a cibiyoyin da ke cikin burane. Ministar kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ita ta bayyana hakan wajen wani taron hadin gwiwan gwamnati. Batun da ya kewaye taron dai shi ne, hanyoyin dakile miliyoyin daloli da ake safarasu.

Gwamnati Za Ta Fara Yi Wa Talakawa Rijistar Tallafin Korona

Ministar ta bayyana cewa, talakawa da mabukatan Nijeriya da ake yi wa rijista za su amfana da tallafin kudade da za a bayar wajen farfado da tattalin arziki sakamakon cutar Korona. Ministar ta bayyana hakan ne a Abuja ta bakin mai mai ba ta shawara ta fannin yada labarai da sadarwa,Yunusa Abdullahi, ya bayyana cewa, za a gabatar da wannan shiri ne domin magance matsalolin da cutar Korona ta haddasa a cikin kasar nan.

Ministar kudi ta bayyana cewa, za a gudanar da wannan rijistan ne ta hanyoyi guda biyu wanda ya hada da na farko da na biyu tare da bayanan asusun banki da kuma bayanan daga hukumar kidaya ta kasa ga masu amfani da wayoyin salula. Domin dakile hanyoyin cin hanci da rashawa, ministar ta bayyana cewa, biyan kudaden zai kasance ne kai tsaye ta asusun bankin mutum wajen yin amfani da BbN.

Minista ta ce, “sakamakon kai dauki ga cutar Korona a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari kamar yadda ya yi alkawari, za a tallafa wa mutane domin rage radaden tattalin arziki, amma wadanda za a tallafa musu dai su ne talakawa da kuma mabukata.”

Karanta: Masu hakar Mai da Gas sun yi asarar Naira Biliyan 320

Ministar ta bayyana wa mahalarta taron cewa, gwamnati ta gudanar da wani tsari na shekarar 2021 zuwa shekarar 2023 kan harkokin kudade da kuma samar da wani tsari wanda a ke tsammanin samun kudade na Naira tiriliyan 2.3 a cikin wannan shekarar da muke ciki. Ta ce, gwamnatin tarayya ta aiwatar da wasu tsare-tsare wadanda su ka hada da bayar da tallafi da ciyar da ‘yan makaranta wanda a yanzu haka yake gudana da kuma samar da tsarin tattalin arziki.
Ta ce, “domin takaita lamarin, domin dakile matsalolin gibin kasafin kudi da ake samu da yin cushe domin cin hanci da rashawa da sauran su, mun samar da wani tsari wanda zai dai-daita harkokin kudade a Nijeriya.

“Wannan photo voltaic hada da samar da kimiyya wanda zai bayar da damar kulawa da kudaden da ake kashewa a cikin tsarin tattalin arziki.”

Ministar kulin ta kara da cewa, cutar Korona ya janyo matsaloli masu yawan gaske wanda suka sa aka dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da harkokin gwamnati da kudade da kaucewa cin hanci da rashawa da samar da gwarin gwiwa a tsakanin gwamnati da kuma ‘yan kasa.

1 COMMENT

What's On Your Mind?