Imam Yau – Gwamnati Ta Zo Da Salon Da Ba Mu Sani Ba

0
67

A kan gunagunin da jama’a da yawa suke yi dangane da kasuwannin da gwamnati ke ta faman rusawa a Jihar Kaduna. Jama’a da dama suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

Gwamnati Ta Zo Da Salon Da Ba Mu Sani Ba Imam Yau

Imam Aliyu Yau Hashim, Limamin Masallacin Juma’a na layin Umaru mai guga titin Abuja, Rigasa Kaduna. Ya yi Magana ne kan wannan lamarin inda yake cewa:

“Muna fatan Allah ya bai wa gwamnati ikon cika kudurin da ta dauka na gina sabuwar kasuwa wacce ta dace da zamani, kamar yanda suka rusa, Allah ya ba su ikon ginawa. Kowa ya sani cewa talakawa bakidaya photo voltaic shiga cikin kunci a garin Kaduna bakidaya ba a Rigasa kadai ba. Gwamnati ta rusa dukkanin kasuwanni, ta zo da sabuwar taswira tana son za ta gina ta zamani, kuma Alhamdu lillahi, kowane zamani yana zuwa ne daidai da lokacinsa, don haka muna rokon Allah ya ba su ikon iyar da nufin gina sabbin kamar yanda suka kuduri aniyar yi.

A yanzun, masu rumfuna da ma wadanda ba su da rumfunan kowa ya shiga cikin halin kunci. Sakamakon a baya mutum yana cikin rumfarsa yana samun abin tasarrufi shi da iyalinsa, amma a halin yanzun kowa ya shiga lalube. Wasu ma laluben kawai suke yi amma sam ba su ma san inda suka dosa ba.

Shugaban Kamfanin NNPC Ya Yaba Wa Kungiyoyin kwadago Kan Janye Yajin Aiki

Wannan shi ya sanya a kullum muke janyo hankulan mutane muna nu na masu cewa gwamnati ba a sukarta, ba a zaginta, gwamnati ana bukatar a tsaya ne a yi mata addu’a, musamman a wannan karni da muke a cikinsa. Wannan gwamnatin ta dauko wani salo ne wanda ba mu san shi ba, kuma alhamdu lillahi ana samun kurakurai a wurare masu yawa, ana kuma samun daidai a wurare masu yawa. Amma muna son wannan salon da wannan gwamnatin ta dauko sport da rumfunan, da ta tsaya ta tantance ta duba, domin bai wa kowa hakkinsa. Sannan kuma ya kamata gwamnati ta sani tsawwala kudin rumfuna ba shi ne samun nasara ba. Gwamnati ta dai tsaya ta taimaki talaka, sai Allah ya taimake su.

Yanzun kuma tsaro ya yi nisa, babu tsaro a cikin kasa, sannan abinci kuma ya yi nisa, a duba dukkanin kayayayyakin abinci, duk photo voltaic yi wa talaka nisa. Kowa kuma ya san wannan halin da ake ciki. Sannan kuma a ce gwamnati ta zo tana tsawwala kudi a kan rumfuna, a gaskiya hakan zai zama ba a yi wa talaka adalci ba, domin ba kowa ne zai sami halin iya saye ba, a karshe kuma duk wahalar a kan talakawan ne dai zai koma.

Dangane kuma da wannan mummunan yanayin na tabarbarewar tsaro da muke a cikinsa, mu muna da tabbacin matukar gwamnati ta kuduri aniyar da ta dace, a cikin dan lokaci kankane komai zai iya daidaita, domin mun san babu abin da ya fi karfin gwamnati a cikin kasarta. Duk abin nan da ake yi sam bai gagari gwamnati ba, ai gwamnati ikon Allah ce. Allah ne ya kafa ta, kuma tana da karfin mulki, tana kuma da karfi ta kowane gefe.

Muna kuma kara yabawa da yin jinjina ga gwamnan Borno, wanda ya nu na cewa tabbas shi jarumi ne, a duk inda ake ta’addanci a cikin Jiharsa, wannan bawan Allah babu inda bai kutsa ba. Da dazuka da kauyukan Jihar Borno babu inda bai je ya kwana ba.

A yanzun kowa ya sani a kasar nan, duk wanda zai ce zai sanya ido a kan abin da ake yi, to tilas ne a kai masa hari, sai dai kuwa in za ka kawar da idonka a kan abin da ake yi, to shi ne zamanka lafiya a kasar nan. Masu ayyukan ta’addancin nan Allah ya karkato mana da zukatansu su daina, gwamnati kuma ta dukufa wajen samar da ayyukan yi, domin muna da tulin matasan da suke zube babu ayyukan yi, rashin aikin yi kuma masifa yake jawowa a cikin kasa.
A karshe ina kara nanata kira ga dukkaninmu da mu dage da ci gaba da addu’a, Allah ya zaunar da kasarmu lafiya.

What's On Your Mind?