Gwamnati Ta Yi Garambawul Ga Wa’adin Samun Fasfon Nijeriya Zuwa Mako Shida

0
129

Gwamnati Ta Yi Garambawul Ga Wa’adin Samun Fasfon Nijeriya Zuwa Mako Shida

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana shirin yin garambawul ga daukacin matakan da ake bi wajen bayar da fasfo a Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) inda mutane za su rika samun fasfonsu a halin yanzu cikin mako shida domin tabbatar da mutunta hakkin dukkan masu neman fasfon.

Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana haka a wani taro da ya gudana tare da Shugaban NIS Muhammad Babandede da sauran jami’an kula da ayyukan fasfo a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Aregbesola ya bayyana cewa, “Mun fuskanci kalubale daban-daban a baya ciki har da karancin littafin fasfo da fama da masu tatsar mutane da dan karen tsada da bai wa wadanda ba su cancanta ba da sauransu. Don haka ya zama wajibi mu sake duba matakan bayar da fasfo mu yi garambawul din da ya kamata domin biyan bukatun abokan huldarmu.”

A cewarsa, shiri ya yi nisa na baza jami’an tsaro na zahiri da badini a dukkan ofisoshin fasfo, “za su sanya kamarori a jikinsu. Za su bankado tare da ba da rahoton duk masu bambadanci da kara farashi da walankeluwa, da tatsar mutane ko karkatar musu da kudi, da boye fasfo da sauran abubuwa na cin hanci da rashawa. Duk wanda aka kama zai dandana kudarsa kamar yadda doka ta tanada,” ya bayyana.

Ministan ya kuma kara da cewa za a samar da kafar da mutane za su rika gabatar da koke-koke da kuma kai rahoton duk wasu jami’ai da suke saba ka’ida.

Ministan ya sake jaddada haramcin dukkan wani nau’i na yi wa masu neman fasfo abubuwan da suka saba ka’ida.

Daga cikin abubuwan da aka tattauna a wurin taron solar hada da kafa cibiyoyin aikin fasfo na hanzari bisa hadin gwiwa da bangare mai zaman kansa inda ake sa ran kafa karin guda 10 cikin ‘yan makwanni masu zuwa a sassan kasar nan baya ga wanda aka bude a Abuja.

Za a rika sanya wa’adi ga kowace bukatar fasfo da aka gabatar ciki har da ranar da za a kammala aikinsa mai shi ya je ya karba. Wa’adin shi ne na mako shida wanda zai ba da damar samun isasshen lokaci na bincken bayanan da mai neman fasfo ya gabatar da kuma tabbatar da cika alkawari.

Haka nan za a tabbatar da bai wajaba ga duk wani mai neman fasfo ya yawaita magana da jami’ai ba in baya ga gabatar da bukatarsa, kana za a rika sanar da mai neman fasfo idan an fuskanci wani kalubale ko idan lokacin karbar fasfonsa ya yi.

Wakazalika a sabon gyaran da za a aiwatar, za a rika wallafa sunayen wadanda aka kammala aikin fasfonsu ba su je solar karba ba, inda za a nemi su tafi babban ofishin NIS na jiha domin amsa.

Ministan dai ya ce bisa wannan sauye-sauye da aka kawo, za a cimma burin da aka tasa a gaba a bangaren bayar da fasfo

A nashi bangaren, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya bayyana cewa taron da aka yi wanda ya kunshi dukkan jami’an kula da ofisoshin fasfo guda 42 da sauran wadanda suke aikin bayar da fasfo a ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke kasashen waje, abin a yaba ne saboda zai karfafa yi wa ‘yan kasa aiki nagari a gida da waje tare da kawar da bata-gari daga cikin ayyukan bayar da fasfo.

Ya kara da cewa, a lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar, ya mayar da hankali wajen inganta aikin fasfo wanda ya kai su ga sadaukar da babban taronsu na shekara ga bangaren fasfo a Jihar Ogun, inda aka gayyaci kwararru domin su yi bita ta tsanaki tare da zakulo kurakuran da ya kamata a gyara da kuma kara inganta fasfon. Bayan haka, bangaren bunkasa ababen extra rayuwa domin jin dadin aiki ga jami’ai da tabbatar da cikar burin umarnin da bangaren zartarwa na tarayya ya bayar na saukaka hada-hadar kasuwanci a cikin kasa duk solar samu tagomashi, kamar yadda mutane za su iya gani a fili a sassan ofisoshi da sansanonin hukumar ta NIS.

Babandede ya nunar da cewa daga nasarorin da aka samu ne aka kaddamar da sabon ingantaccen fasfo na zamani wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Janairun 2019.

Sauran abubuwan da aka inganta fasfon da su, su ne kara wa fasfon alamomi na tsaro, da kara yawan tambarin yatsu da ake dauka daga guda hudu zuwa goma, sanya lambar shaidar zama dan kasa da shigar da kowane fasfo cikin rumbun bayanai don tabbatar da wani bai yi fasfo biyu ba. Haka nan an samu nasarar shigar da bayanan fasfo da suka bace ko aka sace a cikin manhajar rundunar ‘yan sandan duniya don hana miyagu amfani da fasfon ta hanyar da ba ta dace ba.

Har ila yau, shugaban na NIS ya ce solar samar da tsare-tsare da suka saukaka matakan neman fasfo ta yadda ‘Yan Nijeriya da ke waje za su iya gabatar da bukatarsu ba sai solar yi takakkiya zuwa ofisoshin jakadanci ba.

Sai dai kuma, CGI Babandede ya bayyana cewa, “Duk da irin kokarin da muke yi na ganin mun samar da isassun takardun fasfo ga ‘Yan Najeriya cikin sauki, ba za mu kauce wa fadar gaskiyar cewa muna fuskantar kalubale da ke kawo mana cikas a aikin ba. Ya kamata a san cewa aikin fasfo na ‘Yan Nijeriya gabadaya kwangila ce da ake biyan kudi ba tare da samar da kudin ruwa ga gwamnati ba.. yayin da kudaden shigar da ake samu a kasashen waje kai tsaye ake zuba su cikin asusun JP Mogan don sake aikawa da kudaden ga gwamnati.”

Shugaban hukumar ya sake nanata kudirin hukumar na tabbatar da ingancin ayyuka ga ‘yan kasa da kuma kawar da bata-gari da za su iya kawo cikas ga kokarin samun nasarar abin da aka tasa a gaba.

A yayin gudanar da taron dai, an bai wa jami’ai daban-daban damar yin jawabai da kuma bayar da gudunmawa kan matakan da suka kamata a dauka don tabbatar da komai ya tafi daidai-wa-daida a ofisoshinsu yayin gudanar da ayyukan na fasfo.

What's On Your Mind?