Gwamnati Ta Amso Bashin Kayayyaki Na Naira Tiriliyan Daya Domin Bunkasa Masana’antu

0
135

Domin farfadowa daga matsalolin tattalin arziki wacce cutar Korona ta haddasa, gwamnatin tarayya ta amso bashin kayayyaki wanda kudinsu ya kai na naira tiriliyan 1, domin bunkasa kayayyakin cikin gida da samar da mahimman fanonin tattalin arziki a matsayin wani bangare na farfado da tattalin arzikin kasar nan. Da take jawabi a wajen taron murnar tashishin bakin teku wanda ya gudana a Jihar Legas, mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin bunkasa cimma muradu, Princess Adejoke Orelope- Adefulire, ta bayyana cewa, akwai shirin samar da bayar da bashi na naira biliyan 100 ga magidanta da kuma kananan ‘yan kasuwa a karkashin hukumar NIRSAL.

Gwamnati Ta Amso Bashin Kayayyaki Na Naira Tiriliyan Daya Domin Bunkasa Masana’antu

A cewarta, an samar da bayar da kudade bashi na naira biliyan 100 ga kamfanonin magunguna da masu sarrafa kayayyakin lafiya, domin bunkasa cibiyoyin harkokin lafiya a cikin kasar nan. Ta yi kira da a hada kai wajen samar da irin wannan lamari ga dukkan sauran bangarorin tattalin arziki, inda za a samu bunkasa tattalin arziki da rage kangin talauci da inganta albarkatun kasa domin samun yin amfani da su nan gaba. Adefulire ta kara da cewa, bangaren tashoshin gabar bakin teku, yana samar da makudan kudade masu yawa da inganta kayayyaki, yana da kyau ya zama cikin tsaro ba wai wajen barazana ga muhalli a Nijeriya ba.
Ta ce, “dole ne mu tallata kayayyakin cikin gida da zuba jari a bangaren kayayyakin further rayuwa wanda zai kawo bunkasa tattalin arziki mai yawan gaske. Yana da matukar mahimmanci mu iya amfani da kayayyakin cikin gida domin magance matsalilin tattalin arziki da karawa masu karkira na cikin gida gwarin gwiwa,” in ji ta.

CBN – Mu Na Samar Da Tsarin Yakar Koma-Bayan Tattalin Arziki

Ta ci gaba da bayyana cewa, yana da matukar mahimmanci a mayar da hankali kan amfani da kayayyaki da aka sarrafa su a kasar nan, domin ta hanyar haka ne kadai za a samu bunkasar tattalinn arziki cikin dan kankanin lokaci.
Mai bai wa shugaban kasan shawara ta kara da cewa, sakamakon matsalolin da aka fuskanta lokacin cutar Korona ya janyo Duniya ta sake sabon tsari a bangaren tattalin arziki da na tafiye-tafiye da yawan bude ido da tashoshin bakin teku da kamun kifi da abincin da a ke samu a bakin teku, dukkan wadannan photo voltaic fuskanci matsaloli wanda ya sa aka samu raguwar tattalin arziki wanda ya kai na kashi 3.5 zuwa kashi bakai a fadin Duniya.

A halin yanzu dai, shugaban gudanarwa a hukumar da ke kula da tashoshin bakin tekun Nijeriya, (NIMASA), Dakta Bashir Jamoh, ya bayyana cewa, hukumarsa ta na kokarin tsaftace bakin tekunan Nijeriya daga ayyukan ta’addanci. Ya bukaci karin hadin gwiwa da jami’an tsaro wajen dakele rashin tsaro a yankunan bakin tekun Nijeriya.

What's On Your Mind?