Gwamnati Na Da Karfin Murkushe Matsalar Tsaron Kasar Nan – Ministan Labarai

- Advertisement -

Gwamnati Na Da Karfin Murkushe Matsalar Tsaron Kasar Nan – Ministan Labarai

Daga Abubakar Abba,

Ministan Yada Labarai da Bunkasa Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya yi bayanin cewa Gwamnatin Tarayya na da karfin da za su murkushe matsalolin tsaron da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da kuma sauran makiyan Nijeriya ke haddasawa.

Lai ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a jihar Legas, inda ya yi watsi da cewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gamsu da yadda yanayin tsaro yake a yanzu a kasar nan.

A cewar Lai, duk daukacin jami’an tsaron, kayan aikin da gwamnatin ta ke da su, gwamnatin na da komai da za ta iya magance rashin tsaro a daukacin fadin Nijeriya.

A taron na manema labarai, Lai ya ci gaba da cewa, “Ba wai wani sabon labari ba ne kowa ya san kasarmu fuskantar kalubale na rashin tsaro “.

Sai dai, Lai ya ci gaba da cewa, “Na karanta wasu bayanai, cewar Gwamnatin Tarayya ta gamsu kuma ba ta san ya yadda za ta shawo kan kalubalen na rashin tsaro ba”.

Ya kara da cewa, wasu ma har solar wuce makadi da rawa na bayar da shawarar kawo karshen mulkin dimukradiyya wanda wannan wata alama ce ta cin amanar kasa.

Lai ya ci gaba da cewa, “ Na zo nan ne yau domin in tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, a yayin da Gwamnatin Tarayya ke sane da kalubalen na rashin tsaro da muke fuskanta a yanzu, da suka hada da, ta’addanci, garkuwa da mutane, ayyukan ‘yan bindiga da kuma rikicin Fulani makiyaya da manoma, zai yi wuya gwamnatin ta ce ta gamsu da yadda lamarin tsaro yake tafiya a kasar da kuma cewa, ta na da komai da za ta iya magance kalubalen”.

Lai ya buga misali da cewa, jami’an soji na da karfin da za su kawo karshen ‘yan kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP da ke kai hare -hare a cikin garuruwa ko a kauyuka, amma saboda gudun kada a yi asarar rayukan al’umma, shi ya sa suke bi a sannu, inda ya kara da cewa, haka kan ayyukan masu garkuwar da mutane ko kuma dalibanfmu ‘yan makaranta.

Lai ya ci gaba da cewa, akasari jami’an tsaron ba su san inda masu garkuwar suke a boye ba, don hakan, dole ne su yi taka tsantsan wajen gudanar da aikinsu don gudun kada su illata yaran da suke kokarin kubutarwa.

“ Babu wata tantama, gwamnati na da yakini kan jami’an tsaron ta wajen magance kalubalen raahin tsaro da muke fuskanta a yanzu kamar ta’addanci, sace mutane, ayyukan ‘yan bindiga da kuma rikicin Fulani Makiyaya da Manoma”.

“ Muna rokon ‘yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami’an tsaronmu goyon baya kan kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro a daukacin fadin Nijeriya”.

Lai ya danganta harin da aka kai a kan jami’an tsaro a yankin Kudu maso Gabas a matsayin kaddamar da yaki a kan Nijeriya.

Sai dai, biyo bayan wannan furucin na Lai, wasu ‘yan Nijeriya solar caccaki Ministan kan wannan furucin na sa, inda suka yi nuni da cewa, ya furta hakan ne kawai domin ya karkatar da hankulan ‘yan Nijeriya daga kan ainahin lamarin da ke a fuskantar kasar.

Solar caccaki Lai ne ta kafafen sada zumunta na zamani, musamman Na Tuwita inda suka kalubalanci Gwamnatin Tarayya da ta watsar da kalaman da Lai ya furta a zahiri, musamman cewarsa Gwamnatin Tarayya na da karfin da za ta iya kawo karshen ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga ba tare da bata wani lokaci ba.

Har Ila yau, rahotanni solar bayyana cewa, a ‘yan kwanakin nan, ‘yan Nijeriya na ganin tasku tare da zama a cikin tsoro da fargaba saboda rashin tsaro, musamman a yankin Arewa Maso Gabas da ‘yan ta’addar Boko Haram suka mayar tamkar fagen daga, inda kuma a yankin Arewa ta Tsakiya, ta zamo fagen da masu garkuwar ke ci gaba da cin karen su ba babbaka tare da kuma ci gaba da artabu a tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma.

Bugu da kari, a yankin Kudu maso Gabas, nan ma masu garkuwar na sheke ayarsu, sai kuma rikicin Fulani Makiyaya da Manoma a Kudu maso Kudu da kuma kazantar ayyukan ‘yan bindiga da sa ce mutane a yankin da kuma rikcin Fulani Makiyaya da Manoma kudu Maso.

Daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka soki furuncin na Lai a kafar ta sada zumunta, wani @larrymulo Mohammed a kafarsa ta twita ya amince da furucin na Ministan cewa, Gwamnatin Tarayya na da karfin magance ‘yan ta’addar, amma yaki yin hakan.

Shi kuwa @omeokachie2 cewa ya yi Gwamnatin Tarayya ba ta san yadda za ta yi amfani da karfin na ta ba.

@samlobaboy kuwa, sukar Ministan ya yi kan tafkawa ‘yan Nijeriya karya, inda ya kara da cewa, dakarun Soji na can a fagen fama, yayin da Lai ke a gida ya na rabar da tallafin Sallah.

Shi kuma @princefaith85 mamaki ya yi da cewa, in har idan gwamnatin na da karfin yakar ‘yan ta’addar to ya hana ta yin hakan, ERwannan abin dariya ne kawai da kuma cin mutuncin rundunar sojin kasa.

Shi kuwa @Babashola8 shawartar ministan ya yi da ya dai furta duk wani furucin da ya san bai ba kwararan hujjojin da zai gaya wa ‘yan Nijeriya.

Shi ma, @Thony_mart ya ce, in har gwamnatin na da karfin hakan shin jira take yi sai an kashe kow a kasar tukunna.

- Advertisement -