Gwamnan Zamfara Ya Jagoranci Cafke ‘Yan Ta’adda 65 Cikin Mako Biyu

- Advertisement -

Gwamnan Zamfara Ya Jagoranci Cafke ‘Yan Ta’adda 65 Cikin Mako Biyu

Daga Hussaini Yero,

A kokarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi karkashin jagorancin Gwamna Bello Mattawalle na yaki da ‘yan ta’adda da ba su yarda da sulhun ba, yanzu haka hadin gwiwa da Rundunar ‘Yan Sanda ta musamma da aka turo daga Abuja, cikin mako biyu ya cafke ‘yan ta’adda 65.

A ranar 21 ga Ramadhan a wajen shan ruwan buda baki da Gwamna Matawalle, ke yi da Kananan Hukumomin Kauran Namoda da Birnin Magaji. A jawabinsa, Gwamna Matawalle ya bayyana nasarorin da ya samu wajen yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga masu ta da kayar baya, Inda ya bayyana na cewa,ya jagoranci jami’an tsaro wajan kamo ‘yan ta’adda a cikin garuruwa 35.

A yanzu haka gwamnatin Jihar, hadin gwiwa tare da rundunar ‘yan sandan ta musamma da aka turo daga Abuja,solar samu kama  ‘yan ta’adda masu manayan laifuka daban – daban talatin harda ‘yan Kasar waje,inji Jami’an hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, a jawabinsa ga manema labarai a shelkwatar rundunar ‘yan sanda a Gusau.

Shi ma a nasa jawabin Kwamishinan Tsaro na Jihar ta Zamfara, Honarabul Abubakar Dauran, ya tabbatar da cewa, Gwamna Matawalle na iyaka kokarinsa wajen ganin ya kare rayukan al’ummar jihar da kuma dawo da dawamamen zaman lafiya a fadin jihar baki daya.

Don haka muke neman taimakon al’ummar jihar wajen cigaba da yin addu’a dan samun nasara kawo karshe wadannan ‘yan ta’adda da suka addabe mu.

- Advertisement -