Gwamnan Neja Ya Tabbatar Da Bullar Boko Haram A Jihar

0
115

Gwamnan Neja Ya Tabbatar Da Bullar Boko Haram A Jihar

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An tabbatar da bullar kungiyar Boko Haram a Kaure cikin karamar hukumar Shiroro tare da kafa tutarsu.
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira sama da dubu uku da suka fito daga karamar hukumar Shiroro da Munya zuwa makarantar faramare ta Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna.
” An tabbatar da alamun bullar kungiyar Boko Haram a yankin Kaure.
” Na ji cewar solar riga solar kafa tutarsu a Kaure, wanda ke nuna cewar solar mamaye yankin, wannan shi ne abinda na ke ta fadawa gwamnatin tarayya ga shi yanzu solar cin ma wannan matsayin wanda ke nuna cewar idan ba a yi hankali ba har Abuja ba za ta tsira ba,” a cewarshi.
Gwamnan wanda ya bayyana matsayin matsalar tsaro a jihar, ya nuna damuwarsa akan halin da mata da yankunan karkaru ke ciki wanda mambobin Boko Haram ke mallake su.
” Solar mamaye yankin, solar kafa tutarsu. An tabbatar min yanzu. Solar karbe matan mutane da karfi,”. Ya kara da cewa.
Gwamnan yace ” Boko Haram suna bukatar anfani da wannan yankin a matsayin gidajen su kamar yadda su ka yi a Sambisa”.
Gwamnan yace halin da ake ciki yanzu yana bukatar hadin guiwar masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewar gwamnati ta dauki mataki kuma ba za ta ja baya ba za ta cigaba da yunkurawa sai ta kawo karshen lamarin.
Yace bai cire tsammani ba daga gwamnatin tarayya, ba zai tsaya jira ba, yace lokaci yazo da jami’an soja zasu dauki matakin amshe yankin.
” Ya kara da cewar ban debe tsammani ba daga gwamnatin tarayya kuma ba zan tsaya jiran kowa ba”, a cewarshi.
Bulus Asu wani mazauni Kuchi a karamar hukumar Munya, yace tun watanni uku a baya an daidaita yankin gaba daya.
Asu yace solar shigo jihar nan ne ta iyakar mu da jihar Kaduna ta hanyar Kapana suna garkuwa da mutane suna yiwa mata fyade.
Ya bayyana Kuchi, Guni da Gini, Chiri, Fuka da Kapana da wasu kauyukan suna fuskantar matsalolin garkuwa da jama’a sama da shekaru uku da suka gabata.
Bulus ya yabawa mai martaba sarkin Minna, Alhaji Umar Faruk Bahago na kulawa da ‘yan gudun hijira da ke makarantar faramare ta IBB, inda ya nemi gwamnatin jihar da ta dauki mataki mai tsari wajen kawo karshen yanayin da mutane suka haddasa shi.

What's On Your Mind?