Gwamnan Neja Ya Sauke Kwamishinan Ayyuka Daga Aiki

- Advertisement -

Gwamnan Neja Ya Sauke Kwamishinan Ayyuka Daga Aiki

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sauke kwamishinan ayyuka da bunkasa ababan extra rayuwa, Injiniya Ibrahim Mohammad Panti daga aiki.
Sakatariyar yada labarai ta gwamnan, Misis Mary Noel-Berje, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Ba a ba da dalilin cire kwamishinan ba, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da albashin jihar.

CPS ta ce, Kwamishinan tsare-tsare, Alhaji Mamman Musa, zai fara aiki a matsayin Kwamishinan ayyuka da ababen extra rayuwa, yayin da Kwamishinan kudi, Alhaji Zakari Abubakar, zai kula da hukumar tsare-tsare recreation da ma’aikatar kudin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Mamman Musa shi ne zai mika kwamitin tsarawa ga Zakari, yayin da Injiniya Ibrahim Mohammad Panti zai mika shi ga Mamman Musa nan take.”

- Advertisement -