Gwamnan Neja Ya Halarci Jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano

0
313

Gwamnan Neja Ya Halarci Jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

Gwamnan Neja kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya, Abubakar Sani Bello ya halarci jana’izar marigayiya Hajiya Maryam Ado Bayero mahaifiyar sarkin Kano da Bichi.

Jana’izar wanda ya gudana a fadar sarkin Kano ya samu halartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ministoci, sarakunan gargajiya ciki da wajen jihar Kano da tarayyar kasar nan da makota.

Bayan kammala jana’izar, gwamna Sani Bello yayi ta’aziya ga iyalan marigayiyar, inda ya nemi su dauki wannan rashin na Hajiya Maryam a matsayin jarabawa da Allah wanda kuma shi ne karshen rayuwarta.

Shugaban gwamnonin arewar ta tsakiya, yace ” Ku dauki hakuri kuma ku yi riko da abinda ta barku da shi lokacin rayuwarta. Babban abinda ya rage maku yanzu shi ne cigaba da yi mata addu’a”.
Gwamnan yayi addu’ar Allah ya sada ta da aljannar Fidausi kuma ya baiwa al’ummar jihar Kano, masarautar Kano, Bichi da Ilorin da ‘yan uwa hakurin jure rashinta.

Marigayiya Hajiya Maryam Ado Bayero ta rasu a kasar Masar tana da shekaru tamanin da shida a duniya, ‘yar sarki ce kuma yar mai martaba sarkin Ilorin Alhaji Ibrahim Sulu Gambari.

Kafin rayuwarta itace matar marigayi tsohon sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero kuma mahaifiyar sarkin Kano na yanzu da Bichi duk a jihar Kano.

What's On Your Mind?