Gwamnan Gombe Ya Sulhunta Rikicin Kabilancin Da Ya Auku A Jihar Kwanan Baya  

- Advertisement -

Gwamnan Gombe Ya Sulhunta Rikicin Kabilancin Da Ya Auku A Jihar Kwanan Baya  

Daga Khalid Idris Doya, Gombe

Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya jagoranci wani babban taron majalisar tsaro da dukkannin masu ruwa da tsaki, a kokarinsa na samar da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummomir Lunguda da Waja da suke karamar hukumar Balanga bayan rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu a kwanakin baya da ya jawo asarar rayuka da dukiya.

Inuwa yana mai kira ga bangarorin wadanda basa ga maciji da juna su rungumi zaman lafiya tare da yafewa juna domin daurewar zaman lafiya da rayuwa mai inganci a kowani lokaci.

Babban Basaraken kasar Waja, Mai Martaba Bala Waja, Alhaji Muhammad Danjuma Muhammad, ya yi wa ‘yan jarida karin haske jim kadan bayan kammala zaman wanda ya shafe fiye da sa’o’i biyar yana gudana a shekaran jiya.

Basaraken ya ce taron wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya kira kuma ya jagoranta, ya haifar da da mai ido, domin kuwa al’ummomin solar amince su mayar da takubban su cikin kube ta hanyar yafewa juna.

Ya ce: “Gwamnan ya jagoranci makamancin wannar ganawa da dama tun faruwar rikicin a watan Afirilun da ya gabata, baya ga tallafi da dama da ya samarwa al’ummomin da abin ya shafa, don haka yau ina farin cikin shaida muku cewa bangarorin biyu solar yafewa juna don samar da jituwa a tsakanin su.”

Bala Wajan sai ya bukaci jama’ar dake gudun hijira daga al’ummomin biyu da sauran wadanda rikicin ya raba da yankunansu su koma gidajen su don ci gaba da rayuwa musamman ma yanzu da damina ta fadi don su samu damar yin noman bana.

“Lokaci ya yi da zamu fahimci cewa muna bukatar juna domin samun ci gaba da dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya faru, don haka ya kamata mu manta da abin da ya faruwa a baya, mu sake farfado da zaman lafiyan da aka san mu da shi.”

Sai ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa kokari da jajircewarsa na samar da zaman lafiya, dama kokarin sauran masu ruwa da tsakin da gudunmowar su ya taimaka wajen cimma wannar nasara.

Taron wanda Gwamna Yahaya ya jagoranta a zauren majalisar zartaswa ta jihar, ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Dr. Manassah Daniel Jatau, da tsofin mataimakan gwamnan jihar biyu; John Lazarus Yoriyo da Mr. Thaanda Rubainu, da tsohon Alkalin-alkalan jihar mai shari’a Hakila Heman, da shugabannin hukumomin tsaro, da hakiman kasar Balanga da sauran shugabannin addini dana al’umma a yankin.

Sakamakon amincewar da shugabannin bangarorin suka yi na cimma zaman lafiya da fahimtar juna a yayin taron,  Gwamna Inuwa Yahaya ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi ya sanar da rage tsawon dokar hana zirga-zirga da aka kakaba wa al’ummomin.

A sanarwa da ya fitar, wanda daraktan yada labaran gwamnan Gombe Ismaila Misilli ya aiko mana, Sakataren Gwamnatin Farfesa Ibrahim Njodi ya ce “An samu ci gaba sport da wata sanarwa dana fitar kan rikicin kauyukan Nyuwar, Jessu da Heme a karamar Hukumar Balanga a ranakun 12 da 13 ga watan Afirilun da ya gabata waNda ya haifar da sanya dokar hana zirga-zairga a kauyukan Nyuwar, da Jessu, da Sikam, da Degri da kuma Kulani, mai girma Gwamna Inuwa Yahaya ya amince da sake dubi kan dokar, daga ta awa 24 ya zuwa daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na protected kuma dokar zata fara aiki ne nan take.”

Sanarwa ta kara da cewa, “Gwamnati tana jaddada bukatar samun zaman lafiya tsakanin al’ummomi, da kuma himmatuwar ta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.”

Sanarwar ta karkare da cewa, “Don haka ana umurtar dukkannin hukumomin tsaro su tabbatar da bin sabuwar dokar da gwamnatin ta jihar ta sanya. To sai dai ma’aikatan da ayyukan su suka zama wajibi za su ci gaba da ayyukan su yadda aka saba.”

- Advertisement -