Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

0
102

Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, nuna matukar takaicinsa kan yadda jama’a ke watsi da hakkokin dake kansu suka koma bin son zuciya ta hanyar giggina gidajen Mai a cikin unguwanni duk da cewa hakan yana tattare da matukar hadari ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Yana mai cewa, ya dace ne kowace gidan Mai da za a gina a ginata a kan layin da ya dace kuma bisa nazarin yanayin muhalli da wajen da za a yi ginin domin kauce wa shiga hakkin al’umma.

Kamar yadda Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan yada labaran Gwamnan ke nakaltowa ta cikin sanarwar manema labarai da ya fita.

Gwamnan yana magana ne lokacin da ya karbi bakuncin mambobin karamin kwamitin Majalisar Wakilai mai sanya ido kan yadda giggina gidajen mai da Iskar Gasoline a cikin unguwanni, karkashin jagorancin shugabansa, Hon. Ibrahim Mustapha Aliyu.

Inuwa na cewa: “Bukatar da muke da ita na bin ka’idoji da tsare-tsaren ci gaba da yana da mahimmanci, duk abin da wannan kwamiti zai yi ina ganin ya zama dole ya ba da fifiko ga bin tsarin da doka ta tanadar na yanka filaye maimakon kowa ya yi ta yin abinda ya ga dama na yanki da kanka.”

Ya shaida wa mambobin Majalisar Wakilan cewa gudanar da ayyukan ci gaba a halin yanzu da gwamnatinsa ke jagoranta ba zai ba da damar wani ya karya ka’ida wajen gina gidan Mai ko Gasoline ba, ko samun wata kafa da ka iya cutar da rayuwar al’umma da dukiyoyin su.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce an kirkiro hukumar samarwa da adana bayanan filaye a zamanance ta Jihar Gombe (GOGIS) ne da sake fasalin hukumar tsara birane don karfafa bin ka’idoji don amfanin jama’ar jihar.

Ya kara da cewa a matsayin Gwamnatinsa ta kawo canji, dokar da ta kirkiro mai lamba 4 wani kwakkwaran mataki ne na tabbatar da bin ka’ida a bangaren tsara birane.

Ya ce an gina gidajen Mai dana Gasoline da dama a cikin garin Gombe ne tsakanin gidaje ko wuraren kasuwanci wanda hakan yake da hatsari ga rayuka da dukiyoyi kamar yadda ake iya gani a wasu jihohin a fadin kasar inda ake samun munanan hatsura sakamakon gina gidajen Mai da Gasoline dake haifar da asarar rayuka da dukiyoyi da yawa.

Ya ce, gwamnatocin da suka gabata basu bada muhimmanci ga kyakkyawan tsarin yanka filaye ba, lamarin da Gwamnan ya ce ba kawai yana barazana ga ka’idojin ci gaba ba ne, har ma yana tauye hakkin hanya da na jama’a kuma hakan ke haifar da rikice-rikice.

Sai ya daura alhakin rashin tsaron da ke addabar kasar nan yanzu kan rashin bin tsari yadda ya kamata, yana mai cewa matsalar cinye burtalolin shanu zuwa mamaye wuraren kiwo da gandun daji su suka haifar da rikice-rikicen manoma da makiyaya da suka rikide zuwa ‘yan fashi, satar mutane da satar shanu.

Ya ce, “Don haka wannan kwamiti yana da matukar muhimmanci kuma muna maraba da ku zuwa Gombe saboda kun equivalent mu a kan hanyar mu ta kawo canji, za mu fara wadannan gyare-gyaren ne saboda mun yi imanin hakan shi ne silan samar da ci gaba mai daurewa kuma mabuɗin zaman lafiya a tsakanin al’ummar mu a jiha da kasa baki daya.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa ba ta da wani zabi da ya wuce ta gyara kura-kuran da aka tafka don kawo ci gaba a jihar wanda hakan shi ne alamar duk wata gwamnati da tasan me take yi, ya kara da cewa jihar za ta ba da hadin kai da goyon baya ga kwamitin don karba da aiwatar da rahoton shi nan gaba.

Tun farko Shugaban karamin Kwamitin na Majalisar Wakilai Hon. Ibrahim Mustapha Aliyu ya ce majalisar ta kafa kwamitin mai mambobi 38 ne bayan korafe-korafen da ‘yan Nijeriya suka yi na rashin bin ka’idoji wajen kafa gidajen man fetur da gas, labarin dake haifar da hatsaari ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya ce an bai wa kwamitin alhakin tantance yadda gidajen mai dana gas ke bin ka’idojin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta kasa (DPR) da kuma Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) a wasu jihohi ciki har da Gombe.

Hon. Ibrahim Aliyu ya godewa Gwamnatin Jihar Gombe bisa karimcin da ta yiwa kwamatin sa sannan ya yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sport da canjin da jihar ta samu a karkashin shirin sa na gina hanyoyin Mora akalla kilomita 100-100 a kowace karamar hukuma, da Shirin Gombe Koriya Shar na “Gombe Goes Inexperienced” (3G a takaice), da kuma ayyukan dinke manyan kwarurruka a ciki da wajen radar Jihar da sauran sassa.

What's On Your Mind?