Gwamnan Gombe Ya Mika Ta’aziyyarsa Ga Masarautar Gombe Bisa Rasuwar Sarkin Zango

- Advertisement -

Gwamnan Gombe Ya Mika Ta’aziyyarsa Ga Masarautar Gombe Bisa Rasuwar Sarkin Zango

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jajantawa Mai Martaba Sarkin Gombe, Dakta Abubakar Shehu Abubakar da sauran iyalan gidan Bubayero bisa rasuwar daya daga cikin ‘ya’yan gidan sarautar, Alhaji Yahaya Abubakar (Sarkin Zangon Gombe).

Gwamnan wanda ya jagoranci manyan jami’an gwamnati zuwa sallar jana’izar marigayin da aka a yi babban masallacin Bubayero, daga bisani ya bi sahun Sarkin na Gombe da sauran dangin mamacin wajen zaman makoki a dakin taron Sarki don yin addu’o’i na musamman ga marigayin.

A sakon sa na ta’aziya da ya fitar ta hannun Daraktan yada labaransa Isma’ila Uba Misilli, gwamnan ya ce an yi babbar hasara bisa ta rasuwar Sarkin Zango,  yana mai cewa rasuwar wata babbar rashi ce ba  kawai ga masarautar Gombe ba, har ma da Jihar Gombe baki daya.

Ya ce “Ina amfani da wannar dama a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe don isar da ta’aziyyata ga Mai Martaba Sarkin Gombe da sauran ‘ya’yan gidan sarautar bisa wannan babban rashi. Muna fatan Allah ya saka masa da Aljannar Firdausi”.

Hakazalika, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya kuma jagoranci tawagar gwamnati don halartar sallar jana’izar Abubakar Bello Tinka, wanda aka fi sani da Ba’a a masallacin Juma’a na asibitin koyarwa na tarayya da ke Gombe.

Wakilinmu ya nakalto cewa marigayi Abubakar Bello Tinka wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin mota a Gombe, kani ne ga jigo a jam’iyyar APC kuma sanannen dan kasuwa, Alhaji Bala Bello Tinka.

A sakon ta’aziyyar da ya mika ga Dakta Bala Tinka da sauran dangin mamacin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana mutuwar ba a a matsayin abin bakin ciki.

“Mutuwar matashi a kananan shekaru irin haka yana da ban tausayi wanda yake da wahalar jurewa, musamman ga dangi da abokansa, amma hukuncin Allah babu kokwanto, muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa kurakuransa, ya shigar da shi jannatul firdaus”.

Gwamnan ya samu rakiyar wasu daga cikin kwamishinonin sa da wasu manyan jami’ai.

- Advertisement -