Gwamnan Gombe Ya Daga Likafar Misilli Zuwa Darakta Janar Kan Yada Labarai

0
32

Gwamnan Gombe Ya Daga Likafar Misilli Zuwa Darakta Janar Kan Yada Labarai

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya amince da daukaka likafan Ismaila Uba Misilli daga babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da ‘yan jaridu (SSA Media) zuwa Darakta Janar kan harkokin yada labarai da hulda da ‘yan jaridu.

Wata Rawa da Ummi Rahab tayi a gurin daukar film din Farin wata ta dauki hankula

Sakataren Gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi wanda ya fitar da sanarwar hakan a shekaran jiya, ya kuma bayyana cewar bayan karin matsayin da aka yi wa Uba, gwamnan ya kuma yi wasu sabbin nade-nade da suka hada da Kabir Ibn Mohammed a matsayin Darakta Janar na Gombe Media Firm (GMC), nade-naden da suka fara aiki nan take.

Har-ila-yau, Gwamnan ya kuma amince da daukaka mukamin wasu masu taimakawa kan yada labarai (SA) zuwa manyan masu taimakawa kan yada labarai tare da turasu wuraren gudanar da aikinsu da suka hada: Jack A. Tasha babban mai taimakawa kan hulda da jama’a da yada labarai (SSA Media) a ofishin mataimakin gwamnan jihar.

Sanarwar ta ce, daga likafan, nade-nade da karin girmar duk photo voltaic fara aiki ne nan take.

Wakilinmu ya nakalto cewa karin girman da gwamnan ya yi wa Uba Misilli bai rasa nasaba da irin himmarsa da kwazonsa wajen kyautata aiki da inganta hulda da ‘yan jarida wanda hakan ya ke haifar da da-mai-ido da jihar ke sahun gaba-gaba wajen yada aikace-aikacen Gwamnan da gwamnatinsa bisa kokarin Uba.

What's On Your Mind?