Gwamnan Borno Ya Soke Kwangilar Ayyukan Gidaje 40 Bisa Rashin Inganci

0
92

Gwamnan Borno Ya Soke Kwangilar Ayyukan Gidaje 40 Bisa Rashin Inganci

Daga Muhammad Maitela,

Bisa dalian rashin inganci, mukaddashin Gwamnan jihar Borno, Umar Kadafur, ya soke kwangilar ayyuka na miliyoyin naira na ‘yan kwangilar ginin gidaje sama da 40 a garin Njimtilo wanda ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Mataimakin gwamnan, ya dauki matakin soke aikin a ranar Asabar a lokacin da yake ziyarar aikin ginin rukunin sabbin gidaje 500, wanda aka tsara kammala su a wannan shekara.

Bugu da kari, wannan shi ne karon farko a kasancewarsa na mukaddashin Gwamnan jihar, a madadin Gwamna Babagana Umara Zulum wanda yanzu haka yana kasar Saudi Arabia domin gudanar da aikin ibada na Umara.

A hannu guda kuma, ya kara da cewa, sama da yan kwangila 40 wadanda wannan lamarin ya shafa da suka kasa tabuka abin a zo a gani a aikin ginin, alhalin wasu yan kwangilar ayyukan su ya doahi kaso 80 cikin dari na matakin kammala wa.

Mukaddashin Gwamnan, kuma shugaban kwamitin sa ido a aikin rukunin sabbin gudajen 500, wadanda suka kunshi kwararrun injiniyoyi don sanya ido wajen gudanar da aikin sabbin gidajen bisa inganci.

Da yake nuna bacin ransa dangane da matakin kammaluwar aikin, ya ce “wasu daga cikin wadannan yan kwangilar solar gaza saboda yadda suka kasa ci gaba da aikin gidajen.”

Har wala yau, ya umurci yan kwangilar musamman wadanda suka kasa mika rahotonsu ga injiniyoyinmu ko wandanda suka kasa ci gaba da aikin, su gaggauta dawo da kudin da aka basu na kama aiki (Mobilization Charges) ga kwamitin.

A hannu guda kuma ya tabbatar da cewa matakin soke kwangilar tasu ya tabbata saboda yadda suka kasa kammala aikin da aka basu na ginin gidajen. Tare da kira ga injiniyoyi masu sanya ido a aikin da cewa su kara kaimi a aikinsu.

What's On Your Mind?